Akwai hanyoyin gargajiya da ake amfani da su, domin jawo hankalin Zuma, wadannan hanyoyi sun hada da gina gidan Zumar, don jawo hankalinta ta sauka a gidan da aka gina domin ita, wanda hakan zai bayar da damar samar da Zumar da za a yi amfani da ita.
Har ila yau, a nan ga wasu hanyoyi sha daya da ake amfani da su a gargajiyance, domin jawo hankalin Zuma:
1- Shuka Nau’ikan Furanni: Ana bukatar a shuka Furanin da aka saba da su, wadanda suka dace da yanayi da irin nau’in kasar noma, domin yin hakan, zai iya bayar da damar jawo hankalin dandazon Zumar a cikin sauki.
2- Shuka Furanni Da Kaka: Shukar Furanin da ake yi a wani lokaci ko wadanda suke shukawa daga shekara zuwa shekara, na bayar da dama wajen janyo hanklin Zuma, su sauka su da kansu, domin samun abincin da za su ci.
3- Samar Da Hanyoyin Tara Ruwa: Zuma na bukatar ruwan da za ta rika sha, saboda haka, ga wanda ke son ya jawo hankalinta, ana bukatar ya samar da wajen tara ruwa a cikin wani Kwami na shan ruwan Kajin kiwo, wanda hakan zai sanya, ita Zumar ta rika zuwa shan ruwan.
4- Kirkirar Wani Yanayi Na Sabo: Samar da wani guri da za a baza Ganye ko kuma amfani da wani Kogon itace, wadanda za su jawo ra’ayin Zumar ta sauka a kai.
5- Gujewa Yin Amfani Da Maganin Feshi: Kada a yi amfani da duk wani nau’i na maganin feshi, wajen jawo ra’ayin Zuma, domin yin hakan zai iya cutar da ita. Kazalika, za kuma a iya amfani da tsarin Lambu wajen jawo ra’ayinta.
6- Shuka Itatuwa Ko Kayan Lambu: Shuka itatuwa ko wasu kayan Lambu mai samar da kamshi, domin Zuma dabba ce mai son kamshi kwarai da gaske, musamman kamshi irin na Fure.
7- Gina Wa Zuma Gida: Ta hanyar gina wa Zuma gida, musamman na itace, hakan zai sa a iya jawo ra’ayinta ta rika sauka.
8- Samar Da Lambu: Ta hanyar samar da Lambu daban-daban da kuma Bishiya, hakan zai iya sanyawa a jawo hankalinta ta sauka a kai, wanda hakan kuma zai sanya ta rika kawo sauran nau’ikan Zuma.
9- Gwama Nau’ikan Ganye: Ta hanyar gwama nau’ikan Ganye daban-daban a cikin Gona, domin kara ingancin kasar nomar hakan zai sanya a jawo hankalinta.
10- Kirara Wasu Kayan Aiki Kamar sheka: Ta hanyar kirkirar wasu kayan aiki, kamar Ganyen Bishiya da kirkirar Sheka, Kiraren Bishiya da sauransu, hakan zai sa a jawo hankalinta.
11- Shuka Nau’ikan Fure: Ta hanyar shuka nau’ikan Fure a cikin Lambunka, hakan zai ba ka damar jawo hankalin Zuma ta sauka a Lambun naka tare da samar maka da Zuma.
12- Kirkirar Lambu Don Jawo Hankalin Zuma: Ga mai son jawo hankalin Zuma, zai iya kirkirar Lambu domin cimma wannan buri nasa a saukake.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp