Sabuwar gwamnatin Amurka ta ayyana matakin ta-baci kan iyakar kasar na kudanci, tare da dakatar da dukkan bakin haure. Batun na bakin haure ya zama wani muhimmin batu na cikin gida, ga sabuwar gwamnatin Amurkar. Sai dai, bisa wani nazari da kafar CGTN ta gudanar kan intanet, masu bayar da amsa sun bayyana damuwarsu game da matakin sabuwar gwamnatin na shawo kan matsalar bakin haure, inda da dama ke ganin ana amfani da batun ne wajen boye batutuwan rashin kyakkyawan shugabanci na kasar.
A shekarun baya baya nan, bisa rarrabuwar kai da siyasa ke haifarwa da kuma wagegen gibin dake akwai tsakanin masu hannu da shuni da masu karamin karfi, shugabanci a Amurka ya shiga wani yanayi mara dadi, inda ake dora laifin kan masu kaura zuwa kasar. Ana yawan kiransu da masu satar ayyukan yi ko kuma ’yan ta’adda.
- Xi Jinping Ya Mika Sakon Gaisuwa Ga Al’umma Gabanin Shiga Sabuwar Shekarar Gargajiya Ta Sinawa
- Li Qiang Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabuwar Firaministar Kasar Mozambique
Cikin wadanda suka bayar da amsa a nazarin, kaso 82.9 sun bayyana shakku game da ikirarin cewa wadanda suka kaura zuwa kasar sun yi mummunan tasiri kanta, inda suka yi imanin cewa, kawai ana amfani da batun ne wajen boye rashin kyakkyawan shugabanci na kasar. Kana kaso 82.6 sun bayyana damuwar cewa, ci gaba da fito na fito tsakanin jam’iyyu biyu na kasar kan batun baki, zai kara ta’azzara rarrabuwar kai tsakanin jama’a.
Sama da mutane 6,178 masu amfani da intanet ne suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24, kan nazarin wanda CGTN ta wallafa a dandalinta masu amfani da harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci. (Fa’iza Mustapha)