Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, ta rattaba hannun yarjejeniya da Hukumar Bayar da Katin Shedar Dan Kasa (NIMC), domin kirkiro da rumbun adana bayanai, don bai wa manoma tallafin aikin noma.
Manufar shirin shi ne, kara habaka fannin aikin noma tare da samar da wadataccen abinci a Nijeriya, hakan kuwa; ya kasance cikin kudurori takwas na Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
- Nazarin CGTN: Tsauraran Manufofin Amurka Na Shan Suka
- Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba
Rumbun, wanda za a yi masa lakabi da yi wa manoma rijista, za a bukaci amfani da daukar bayanan manoman, domin gano sahihan manoman da za su amfana da tallafin tare kuma da tabbatar da ganin sun mallaki gonaki.
A kashin farko na shirin, ana sa ran yi wa manoma miliyan biyu rijista cikin wata uku, inda kuma za a yi wa kashi na biyu su kimanin miliyan shida rijistar.
A cikin wata uku, Hukumar ta NIMC, za ta iya samun bayanan manoman tare da hada rukuni don cimma burin gudanar da shirin.
Har ila yau, don hukumar ta samu damar isa ga manoman wajen gudanar da shirin, za ta yi hadaka da kamfanoni masu zaman kansu tare kuma yin aiki da sauran ofisoshiinta da ke daukacin kanannan hukumomin wannan kasa.
Shirin ya kuma kunshi amfani da bayar da katin da za a yi amfani da shi, domin cire kudin tallafin noma ga manoman.
Babban Ministan Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Abubakar Kyari, ya bayyan haka ne a jawabinsa wajen taron rattaba hannun wannan yarjejeniyar da aka gudanar a shalkwatar ma’aiktar, ranar Laraba a babban birnin tarayya Abuja.
“Abin da muka rattaba hannun a halin yanzu da hukumar kasa da kasa shi ne, bunkasa yi wa manoma rijista”, in ji Kyari.
Kazalika, ya kara da cewa; za mu yi amfani da manhajar rumbun adana bayanai na Hukumar NIMC, domin samar da katin shedar dan kasa (NIN), tare kuma da sama wa manoman katin da zai dauki bayanansu.
“Da farko dai, za mu gano gonakin da manoman suka mallaka tare da yin nomansu, wanda hakan zai ba mu damar sanin gonakin da suke nomawa, domin yi su rijistar”, a cewar Kyari.