Cikin muhimmin jawabin da ya gabatar ga taron kungiyar BRICS da aka yi ta kafar intanet, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana kudurin kasarsa na yayata batun gina tattalin arzikin duniya ta hanyar yin komai a bude.
Ya ce a matsayin babban dandalin baje koli a fagen cinikayyar hidimomi, baje kolin CIFTIS dake karatowa zai zama wani karin muhimmiyar dama da duniya za ta ci gajiyar manufar bude kofa ta kasar Sin.
Wani nazari da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar tsakanin masu amfani da intanet ya nuna cewa, kaso 93.2 na wadanda suka bayar da amsa na cike da fatan ganin bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na bana wato CIFTIS, suna kuma fatan za a ci gajiyar damarmaki ta hanyar yin komai a bude, da samun moriyar juna da karawa tattalin arzikin duniya kuzari.
Bikin CIFTIS na bana zai samu halartar kasashe da hukumomin kasa da kasa sama da 70, inda kamfanoni 2,000 za su baje koli. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp