Kasar Sin ta karbi bakuncin wani taro da ya gudana tsakaninta da kasashen Rasha da Iran, jiya Alhamis a birnin Beijing, don gane da lalubo hanyoyin warware batun nukiliyar Iran.
Bisa wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar tsakanin masu amfani da intanet a fadin duniya, wadanda suka bayar da amsa na ganin taron na Beijing a matsayin yunkuri mai ma’ana dake da nufin inganta samar da mafita a siyasance kan batun nukiliyar Iran, inda suka yabawa kasar Sin din game da kyakkyawar rawa da take takawa game da lamarin.
- Kalaman Lai Chin-te Na Shan Suka A Fadin Taiwan
- Yawan Cire Haraji Ya Sa Albashinmu Babu Albarka – SSANU
Kimanin shekaru 10 da suka wuce, Iran da Amurka da Rasha da Sin da Birtaniya da Faransa da Jamus, suka cimma yarjejeniyar nukiliyar Iran. Sai dai daga baya, Amurka ta yi gaban kanta wajen janyewa daga yarjejeniyar a shekarar 2018, tare da sake kakaba takunkumai da matsawa Iran, lamarin da ya sake haifar da shakku don gane da batun nukiliyar.
Cikin nazarin, kaso 87.6 bisa dari na masu bayar da amsa sun ce yarjejeniyar muhimmiyar nasara ce ta tafiyar da batutuwa masu muhimmanci ta hanyar tattaunawa, kuma ya kamata dukkan kasashe su yi biyayya da ita maimakon soke ta da sake wata sabuwa. Kaso 89.8 bisa dari na ganin aiwatar da ra’ayi na kashin kai wajen kakaba takunkumai da barazanar amfani da karfi da matsin lamba ba za su taimaka wajen warware batun ba. Kaso 89.5 bisa dari kuma sun yi amanna cewa tattaunawar siyasa da diplomasiyya bisa mutunta juna, ita ce kadai hanya kuma zabi mai ma’ana ta warware batun nukiliyar Iran. Wasu kaso 90.6 bisa dari kuma sun yi kira ga dukkan bangarorin da batun ya shafa su kauracewa daukar matakan da ka iya ta’azzara yanayin da ake ciki, kuma su samar da kyakkyawan yanayi da sharadin samar da mafita ta hanyar diplomasiyya.
Nazarin wanda dandamalin CGTN na harsunan Igilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci suka wallafa, ya samu jimilar mutane 7,766 da suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayinsu cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp