ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

by Bello Hamza
1 year ago
Nijeriya

Shafin harkokin hulda da kasashen wajen Nijeriya a karkashin mulkin Shugaba Bola Tinubu ya bude fagen harkokin kasuwanci da muhimman kasashen duniya ta hanyar amfani da akidar nan ta 4D wanda take ba da muhimmanci ga mutunci Nijeriya da kuma kare muradun ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje.

Akidar nan ta 4D (Hulda da kasashe waje, Samar da ci gaba, Bunkasar Dimokradiyya da kuma Lura da jin dadin ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje) ya samu ne domin karfafa shirin Shugaba Tinubu na ‘Renewed Hope Agenda’ duk kuwa da matsaloli da kalubalen da kasar ke fuskanta.

  • Ministan Wajen Sin Ya Tayawa Takwaransa Na Najeriya Murnar Kama Aiki Ta Wayar Tarho
  • Ma’aikatar Kasuwancin Sin: Dole Ne Amurka Ta Daina Dora Laifi Kan Sauran Kasashe

A ‘yan kwanakin baya Nijeriya ta dauki muhimmin mataki domin karfafa dangantaka da hulda da kasa Jamhoriyar Cuba a bangaren abin da ya shafi kasuwanci da zuba jari a inda kasashen biyu suka sanya hannu a kan yarjejeniya hafintar juna (MoU) domin cimma wannan buri wanda aka tabbatar zai amfani kasashen biyu.

ADVERTISEMENT

Ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar da takwararsa na kasar Cuba, Bruno Rodríguez Parrilla suka sanya hannu a madaddin kasashen biyu, yarjejeniyar za ta mayar da hankali ne a bangaren abubuwan da suka shafi ilimi, kiwon lafiya da musayan al’adu. Ana fatan shirin zai karfafa danganta a tsakanin kasashen biyu.

Nijeriya da Cuba na da dadadden tarihin dangantaka tsakaninsu na tsawon shekaru da dama, sun kuma jaddada aniyarsu na bunkasa bangarorin da suka yi musharaka a tsakanin kasashen biyu.

LABARAI MASU NASABA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Minista Tuggar ya bayyana cewa, kasar Cuba ta taka mihimmiyar rawa wajen samar da ‘yancin kai ga wasu kasashen Afrika a lokacin da ake gwagwarmaryar kwato ‘yanci daga ‘yan mulkin mallaka a shekkarun 60s, 70s, 80s da 90s.

“Cuba da Nijeriya sun yi aiki tare wajen yaki da ‘yan mulkin mallaka a kasashen Angola, Namibia, Afrika ta Kudu da Zimbabwe” in ji shi, ya kara da cewa, wannan sabon yarjejeniyar za ta karfafa hadin kai a bangarorin kimiyya da fasaha, bincike da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

A nasa tsokacin, Ministan harkokin waje na Cuba, ya ce, dangantakar da ke tsakanin Cuba da Afrika mai karfi ne, ya kuma gode wa Nijeriya a kan goyon bayan da ta bata a lokacin da Amurka ta sanya wa kasar takunkumin karya tattalin arziki.

Amma kuma yana da muhimmanci a fahimci cewa, fiye da shekara daya kenan Nijeriya bata nada cikakken ambasada ko wani wakili a kasar ta Cuba, hakan kuma yana matukar shafar harkokin huldar diflomasiya dana kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

A taron manema labarai na shekara-shekara (2025), da ma’aikatar harkokin kasashen waje ta yi kwananan, Minista Tuggar ya bayyana wa Duniya yadda ya tafiyar da harkokin ma’aikatar hulda da kasashen duniya, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta yi nisa wajen nada ambasadoji a kasashen duniya domin tuni sunayen wadanda za a nada yake a gaban majalisar dattawa domin amincewa.

Tuggar, wanda ya yi jawabi mai taken “Nasarori da kalubalen hulda da kasashen waje a karkashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu”, ya kuma bayyana cewa, Nijeriya na aiki tukuru wajen gudanar da harkoki da kasahen waje ta hanyar la’akari da mutunci da kuma jin dadin ‘yan Nieriya a kasashe waje da kuma dawo da mutumcin Fasfot din Nijeriya a sassan duniya.

A wani bangaren kuma, kokarin Nijeriya na bunkasa tattalin arzikin kasa, ma’aikatar harkokin kasashen waje ta samo wa Nijeriya jarin Dala Biliyan 14 daga kasar Indiya, za a zuba jarin ne a bangarori da daban-daban na rayuwa da tattalin arzikin kasa haka kuma kasar Netherlands ta zuba jarin Fam miliyan 250 a bangarori daban-daban na tattalin arzikin Nijeriya.

A nasa tsokacin, tsohon Ambasadan kasar Jamus a Nijeriya, ya bayyana cewa, “An samu fiye da kashi 300 na wadanda suka yanki hannun jarin Nijeriya ‘Eurobond’. Wannan kuma alama ce na yadda duniya ta amince tare da rungumar Nijeriya domin gudanar da harkokin kasuwanci, tuni Nijeriya ta sanya hannu a yarjejeniya kasuwanci a tsakaninta da kasashen Jamus, Saudi Arabia, China, Ekuatorial Guinea, Faransa, Cuba, Katar, Birtaniya India, da kuma Brazil wanda hakan ya karfafa bangaren samar da wutar lantatrki, man fetur aikin gona da kuma samar da ayyukan yi ga dinbin matasan mu.”

Haka kuma masana sun bayyana cewa, tattaunawa da kasa Sin ya bude kofofin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu ya kuma katse dukkan tarnakin da yake kawo cikas a harkokin kasashe biyu a baya. A halin yanzu an fara wata gaggarumar kasuwancin Kashu a tsakanin kasashen biyu an kuma kafa wata kwamiti domin samar da kyakyawar kalkibla domin samun nasarar hulda da juna a tsakanin kasashen. Haka kuma an samar da wata yarjejeniya a tsakanin kasar Ekuatorial Guinea, yarjejeniya nada nufin samar da butun gas tare da bunkasa yankin kahon Guinea gaba daya.

Duk da muhimmanci kasuwanci da zuba jari ga rayuwar kasa, a ‘yan shekarun baya an bata sunan Nijeriya saboda ayyukan rashin gaskiya da wasu ‘yan Nijeriya ke aikatawa a kasashe waje.

Amma a halin yanzu, Minista Tuggar ya bayar da tabbacin cewa, wannan gwamnatin za ta yi dukkan mai yiyuwa don farfado da mutumcin kasar nan tare da kuma kare mutumcin ‘yan Nijeriya a kasashe waje. Ya ce, ‘’muna fatan samun kasar da dukkan ‘yan Nijeriya za su shiga kowacce ofishin jakadanci ko filin jiragen sama ko kuma shiga wata yarjejeniyar kasuwanci ba tare da wani tsoron barazana ba.

“Ka sawwala Nijeriyar da farfot dinta ke bude wa ‘yan kasa kofofin kasuwanci a dukkan fadin duniya kuma a cikin mutuntawa.”

Duk da muhimmancin wadannan matakai da ake kokarin dauka da kuma wadanda aka dauka, ba za su yi wani tasiri ba har sai matakan sun kai ga bunkasa rayuwar al’ummar kasa, kasar da ke fama da dimbin marasa aikin yi da kuma hauhawar farashin kayan abinci dana makamashi.

Masu lura da al’amurran yau da kullum sun jinjina wa Ministan harkokin kasashen wajen Nijeriya a kan yadda ya tsayu wajen daukaka suna da mutuncin Nijeriya a idanun duniya.

Nijeriya
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Ne Afirka Ta Zamanantar Da Sufurin Jiragen Ruwa —Ɗantsoho
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Yadda Oyetola Ya Ƙaddamar Da Babban Taron Ƙungiyar  PMAWCA A Legas
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Lokaci Ya Yi Da Matasan Nijeriya Za Su Ƙwato Ƙasarsu — Kwamred Yahaya Abdullahi
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kamfanin Dangote Na Kara Karfafa Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Jihar Neja

MASU ALAKA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
Manyan Labarai

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro
Manyan Labarai

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya
Manyan Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

June 3, 2026
Next Post
Matatar Mai: Har Yanzu ‘Kabal’ A Ɓangaren Mai Na Yaƙar Nasararmu – Dangote

Matatar Mai: Har Yanzu 'Kabal' A Ɓangaren Mai Na Yaƙar Nasararmu – Dangote

LABARAI MASU NASABA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.