Wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, wanda mutane 15,257 daga fadin kasashe 38 suka bayar da amsa, ya bayyana cewa manufar sanya muradun Amurka gaba da komai tana da mummunan tasiri kan dangantakar Amurkar da Turai, yayin da adadin wadanda suka aminta da Amurka daga kasashe kawayenta daga cikin masu bayar da amsa a nazarin, ya ragu.
A cewar nazarin, kaso 62.9 na masu bayar da amsa sun yi Allah wadai da manufar sanya muradun Amurka gaba da komai, inda suka soki manufar suna cewa, ta yi watsi da hakkoki da muradun sauran kasashe. Adadin wadanda suka bayar da wannan amsa daga nahiyar Turai ya kai kaso 67.7.
Baya ga haka, kaso 55.1 na masu bayar da amsa sun yi ammana cewa Amurka ta gaza wajen sauke nauyin dake wuyanta a matsayinta na babbar kasa ta fuskar tafiyar da harkokin duniya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp