Hukumar kula da Kwalejojin Ilimi a Nijeriya (NCCE) ta rufe tare da kulle cibiyoyin ilimi guda 41 da ke bada shaidar karatun ilimi ta NCE na bogi a jihar Bauchi.
A wata wasika da hukumar ta aike wa kwamishinan ilimi na jihar Bauchi Dakta Aliyu Usman Tilde Mai dauke da kwanan wata 5 ga watan Satumba 2022 da wakilinmu ya ci karo da ita a ranar Laraba, na cewa dukkanin cibiyoyin ilimi da Kwalejojin da lamarin ya shafa an ba su wata daya tak da su tabbatar sun kulle ko kuma su fuskanci shari’a.
Wasikar wacce babban sakataren hukumar mai cikakken iko na NCCE, Farfesa Paulinus Chijioke Okwelle ya sanya wa hannu, ya yi tilawar cewa a watan Oktoba da Nuwamban 2021 hukumar ta gudanar da wani atisayen zagayen kwalejoji a fadin kasar nan domin bankado makarantun da ke bada shaidar kammala karatun NCE na bogi, inda a bisa hadin kai jihohi aka samu nasarar gudanar da aikin binciken cikin nasara.
A cewar hukumar NCCE an tura wa ma’aikatar ilimi ta tarayya rahoton aikin binciken da aka gudanar sannan kuma aka bai wa hukumar umarnin ta gaggauta kulle dukkanin cibiyoyin da ta gano na bogi ne.
“Kan wannan, hukumar nan tana jawo hankalin Gwamnatin jihar Bauchi da ta taimaka mana wajen tabbatar da wadannan makarantun sun kasance a kulle da suke bayar da shaidar NCE na bogi,” Okwelle ya kara.
NCCE ta jero sunan kwalejoji da cibiyoyin ilimin da wannan kullewar ta shafa da aka gano suna gudanuwa ta haramtacciyar hanya da cewa su ne kwalejin ilimi Mayo Belwa da ke hadin guiwa da kwalejin ilimi ta Azare; kwalejin ilimi ta Abubakar Adamu Mu’azu da ke Boto; Al-Iman College of Education, Nasarawa. Nasarawa, Bauchi, da kwalejin ilimi ta Apex da ke Liman Katagun, Bauchi.
Sauran sun kunshi kwalejin ilimi da ke Bununu a karamar hukumar Tafawa Balewa; kwalejin ilimi mai zurfi da ke Magama, Gumau, Toro; kwalejin koyar da ilimin larabci da addini da ke Toro; kwalejin SACH da ke Bauchi, makarantar koyar da ilimin Kimiyyar lafiyar muhalli (EHS) da ke Bauchi; kwalejin ilimi ta ECWA da ke Bayarw da kuma cibiyar ilimi ta Garba Ibrahim.
Cibiyoyin ilimin da rufewar ta shafa har da cibiyar koyar da ilimin addini da larabci ta Murkazul Islam da ke Azare; Azare Sahib College of Education; kwalejin ilimi ta Sardauna da ke Bauchi; kwalejin ilimi ta Sheikh Adamu Abubakar da ke Azare; Sunnah Bauchi College of Education, Toro; Thomas Moor Institute, Bauchi; Urat Memorial College of Education, Bauchi; Diamond Teachers Training College of Education, Bauchi da kuma kwalejin ilimi ta Ibrahim Bello da ke Magama Gumau.
Sauran sun hada da kwalejin ilimin addini da larabci ta Annur Kano da ke Bauchi; kwalejin ilimin addini da larabci ta Annur Kano da ke karamar hukumar Katagum; kwalejin ilimi da ke Burra Ningi; Annur Kano College of Education, Giade; kwalejin Sheikh Adam, Azare, Bauchi; Annur Kano College of Education da ke karamar hukumar Warji; Da’awa Bauchi College of Education, Darazo; Da’awa Bauchi College of Education, Kafin Kafin Madaki, Bauchi; Danyaya College of Education, Miya Ganjuwa Miya Ganjuwa LGA, Bauchi; Darazo College of Education, Akuyam; Gindiri College of Education, Warji LGA, da kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi Kumbotso Gidan Marayu Katagum Zaki.
Farfesa Okwelle, “Dangane da wannan matakin, kwalejoji da cibiyoyin da lamarin nan ya shafa suna da zarafin wata daya da su kulle ko su fuskanci shari’a.”
LEADERSHIP ta yi tilawar cewa a watan July na 2021 Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta nuna damuwarka kan cibiyoyin da aka gano suna bada shaidar kammala karatun NCE na bogi a jihar.
A kudirin da mambar Majalisar mai wakiltar mazabar Hardawa, Hon. Mohammed Babayo ya gabatar, ya ce wannan lamarin na shafan harkar ilimi a jihar tare da gurbata sashin ilimi.
A cewarsa, cikin kwalejin ilimi masu zaman kansu guda 58 da ke bada shaidar kammala NCE, guda 13 ne kacal suke da rijista da NCCE.
Majalisar ta bukaci Gwamnatin jihar Bauchi da ta tuntubi hukumar NCCE da hukumar NBTE domin lalubo bakin zaren dakile makarantun da suke bada shaidar NCE na bogi a jihar.
A cewarsa, “Akwai bukatar cikin gaggawa a shawo kannwan matsalar domin tsarkake harkokin ilimi.”
Nan take, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Y Sulaiman ya umarci kwamitin Majalisar na ilimi da ya bincike lamarin sannan ya gabatar musu da rahoto cikin kwanaki 30.