Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta bayyana cewa tana neman mai otal din Adekaz, Alhaji Ademola Afolabi Kazeem (wanda akafi sani da Alhaji Abdallah Kazeem Muhammed) ruwa a jallo kan laifukan da suka shafi safarar miyagun kwayoyi da badakalar kudade a jihar Legas.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya ce, an yanke hukuncin bayyana wanda ake zargin ne ruwa a jallo biyo bayan gazawar sa na amsa gayyatar hukumar ta NDLEA da kuma umurnin da wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta ba hukumar a ranar Litinin 17 ga Oktoba, 2022.
Adekaz ya kasance wanda ke daukar nauyin wasu masu safarar miyagun kwayoyi da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kama a yunkurinsu na fitar da hodar iblis a baya-bayan nan zuwa Dubai da Hadaddiyar daular Larabawa UAE da sauran wasu kasashen wajen Nijeriya.
NDLEA ta kuma ce ” jim kadan bayan kama daya daga cikin yaransa, Bolujoko Muyiwa Babalola, direban kamfanin motar BRT a Legas a ranar 27 ga watan Yuni a filin jirgin sama na Murtala Muhammed MMIA, Ikeja, Alhaji Kazeem wanda kuma shine shugaban kamfanin Adekaz Global Integrated Services. ya bata-bat.”