Hukumar dakile safaran miyagun kwayoyi (NDLEA) ta cafke wata mata mai juna biyu da wata uwa mai jego da wata dalibar jami’a ‘yar aji biyu kan safaran miyagun kwayoyi.
Hukumar ta NDLEA ta ce, wadanda ake zargin su na daga cikin mutum 28 ne da ta kama da tabar Wiwi mai nauyin kilogiram 9,437.7 da tabulet din maganin opioids da sauran miyagun kwayoyi a samamen da ta gudanar a jihohin 12 da suka kunshi: Yobe, Ondo, Edo, Rivers, Akwa Ibom, Imo, Jigawa, Kogi, Adamawa, Kaduna, Kwara, Lagos da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi a FCT, ya ce, dakarunsu a ranar Asabar 15 ga watan Oktoba sun mamayi wani kauye mai suna Chukuku, mai nisan kilomita 10 da Gwagwalada inda suka gano wani katafaren rumbun boye tabar Wiwi.
Inda aka kamo jumbo 510 na haramtattun tabar masu nauyin kilogiram 5, 640 tare da cafke wata mata mai shayarwa Sa’adatu Abdullahi, ‘yar shekara 35, da take kula da rumbun.
A jihar Yobe kuwa hukumar ta kama kilograms na tabar Wiwi 48 a Buni Yadi, kuma sun mamayi wani wuri da ke Potiskum inda suka kamo kilograms na tabar 31 daga wajen mutum biyu da ake zargi Mohammed Mamuda da wata matar aure mai juna biyu, Hauwa Haruna.
Kazalika, wata dalibin jami’ar karatu daga gida (NOUN) da ke karanta ilimin aikin jarida, Ms. Mercy Nyong, ‘yar shekara 30 a duniya, a ranar Laraba 12 ga watan Oktaba.ne ta fada tarkon hukumar a filin sauka da tashi na Jirgin saman kasa da kasa ta Murtala Muhammad da ke Ikeja, Legas a kokarinta na fita da garam 300 na Tramadol samfurin 225mg cikin abun boye turare zuwa Dubai.
Sannan wasu ‘yan kasar Ghana su 9 an cafke su a kokarinsu na yin safaran kilograms 10,843.95 na tabar Wiwi ta tekun Nijeriya, inda kuma a ranar Juma’a 14 ga watan Oktoba aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara 72.
Da fari dai jami’an hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC ne suka kama su kana suka mikasu ga hukumar NDLEA domin fadada bincike da gurfanar da su.
A karshe dai an gurfanar da su a kotu kan kara mai lamba FHC/L/292C/2021.
Da yake yanke hukunci a ranar Juma’a, Mai Shari’a Akintayo Aluko na babban kotun tarayya da ke Legas ya kama tare da daure ‘yan Ghana din bisa safaran Wiwi inda ya daure kowannesu shekara takwas a gidan yari.
Wadanda aka dauren su ne: Victor Wuddah; Freeman Gazul; Adotete Joseph; Sottie Moses; Sottie Stephen; Christian Tette; Kanu Okonipa; Daniel Koyepti; da Kanu Natte.