Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), a Jihar Kaduna sun kama mutane dubu daya da dari biyu da talatin da biyu (1,232) da kuma kilogiram 15, 104.555 na haramtattun miyagun kwayoyi.
Ibrahim Baraje, Kwamandan NDLEA na jihar ne, ya bayyana cewa an kama mutanen tare da kwato miyagun kwayoyi daga watan Janairu zuwa Disamba 2022.
- Mutum 18 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Bauchi
- Al’ajabi: Yadda Mata Da Miji Suka Rasu Akan Gadon Aurensu A Kano
Ya ce mata 68 da manya maza 1,163 na daga cikin adadin wadanda ake zargin.
Ya yi bayanin cewa tabar wiwi mai nauyin kilo bakwai 432.942kg, sai hodar iblis mai nauyin kilogiram 234.653.
Baraje ya kara da cewa an yanke wa mutane 199 hukunci yayin da ake ci gaba da shari’ar mutum 350 sannan an yi wa mutane 683.
Ya ce, “An lalata gidajen haramtattun kwayoyi 132 sannan an rufe kadarori 27 da ke da alaka da masu safarar miyagun kwayoyi.”
Kwamandan ya bayar da tabbacin cewar NDLEA ta jajirce wajen yaki da miyagun kwayoyi da kuma shan su, inda ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta tabbatar da cewa duk masu aikata laifin sun fuskanci fushin doka.
Baraje ya yi kira ga mazauna garin da su rika bai wa rundunar bayanai masu amfani a koda yaushe domin ta samu damar gudanar da aikinta yadda ya kamata.
Ya kuma shawarci masu irin wannan aika-aika da su samu ingantacciyar hanyar rayuwa domin sana’ar miyagun kwayoyi ba za ta kai su ko ina ba.