Humar hana sha da fataucin miyagun kwayoui, ta kama mutum 761 da ake zarginsu da safarar miyagun kwayoyi da kuma kwace kiligiram 11,000 na haramtattun magunguna a jihar Kaduna a watanni takwas daga farkon wannan shekarar.
Shugaban hukumar na jihar Kadunan Mista Umar Adoro, ne ya bayyana haka ga Kamfanin dillacin labarai na Nijeriya a Kaduna.
Ya ce, mutum 610 cikin wadanda aka Kaman masu shan kwaya ne, mutum 480 daga cikinsu an tsare su ana kokarin kawar da su daga shaye-shaye.
“Mun kama mutum 151, mutum 69 na hannun jami’an tsaro, mutum 82 na gaban alkalai,’’ in ji shi.
Kamar yadda ya ce, daga cikin abubuwan da aka kwace har da tabar wiwi da kuma wasu magunguna da ake anafani da su wajen maye.
Adoro ya ce, yaki da shan miyagun kwayoyi abu ne wanda ke bukatar hadin kan al’umma, saboda haka hukumar ta NDLEA ta bukaci a’umma su bayar da gudummowa wajen ganin an samu nasara.
“Za mu ci gaba da yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a dukkan fadin jihar Kaduna’’ kamar yadda Adoro ya tabbatar.
NIS Ta Kubutar Da ‘Yar Shekara 13 Daga Masu Safarar Kananan Yara A Kebbi
Shugabar hukumar kula da shigi da fici (NIS), ta jihar Kebbi Misis Rabi Bashir Nuhu,ta ce hukumar ta su ta samu nasarar kubutar da wata yarinya mai shekara 13, mai suna Temitope Marbellous daga masu safarar mutane.
An mika yarinyar ga hukumar da ke yaki da safarar mutane a kan iyakar Koko wadda ake bi daga jihar Ogun zuwa Sakkwato a keta ta jihar Kebbi.
Da take bayani bayan mika yarinyar ta ce, wadda aka Kaman ta fadi wasu wurare a kasar Libiya, da ake kai mutanen da aka dauka.
Haka kuma ta ce an sanu adireshin wadansu mutane a hannunta wadanda ke zaune a kasar Libiya wanda hakan ya dada tabbatar da cewa za ta kai yarinyar kasar ta Libiya ce.
Yarinyar ta ce an ce za a kai ta Libiya ne ta samu aiki, wanda kuma sai daga baya ta fahimci ba gaskiya ba ne. Sai ta fahimci cewa za a kai ta don a saka ta karuwanci ne.
Nuhu ya jaddada cew, hukumar ba za ta zura ido ba ta bar wasu mutane suna ci gaba aikata laifukan da suka shafi safarar nutane ba.
Shi ma a nasa jawabin shugaban hukumar ta NAPTIP da ke kula da jihar Sakkwato Rilwan Mohammed Buhari,ya ce, su ma za su kara zage dantse wajen ganin sun yaki wannan mummunar sana’a ta safarar mutane.