Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta cafke wani dan kasuwa, Paul Okwuy Mbadugha da safarar hodar iblis zuwa kasar Vietnam a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe (NAIA), Abuja.
An kama wanda ake zargin mai shekaru 54 a yayin bincike a filin tashi da saukar jiragen sama na Abuja a ranar Litinin 12 ga watan Agusta, 2024 yana kokarin tashi a jirgin Qatar (QR 1432) zuwa Hanoi, Vietnam.
- Shin Usman Abdalla Zai Iya Dawo Da Martabar Kano Pillars?
- Kawar da Shaye-Shayen Tamkar Kawar da Miyagun Laifuka Ne – Kwamandan NDLEA Na Kebbi
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce, bayan kwanaki hudu ana gudanar da bincike, an fahimci Mbadugha ya hadiye kullin hodar iblis guda 88 wanda nauyinta ya kai kilo 1.710.
A cikin bayaninsa, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa, shi dan kasuwa ne da ke Legas, cewa wani abokinsa ne ya ba shi hodar Iblis din domin safararta zuwa kasar Vietnam a kan kudi dala 2,000.