Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Katsina ta kama wadanda ake zargi da ta’ammuli da miyagun kwayoyi akalla mutum 345 a fadin jiha tun daga watan Janairu har zuwa watan Mayun wannan shekara.
Kwamandan hukumar, Muhammad Bashir Ibrahim ya sanar da haka a wajen bikin rana yaki da shan miyagun kwayoyi ta duniya na bana wanda za a kwashe mako daya ana gudanarwa.
Ya ce akalla an saita wa mutane masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi tunani su kimanin 388 a wannan dan tsakanin.
Haka kuma hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi a Jihar Katsina ta shirya wani taron kara wa juna sani na wuni daya a kan rawar da jami’ai za su taka wajen yaki da fataucin miyagun kwayoyi tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
Taron kara wa juna sanin ya gudana ne a hedikwata hukumar da ke Jihar Katsina
Hakazalika, Ofishin hukumar NDLEA na shiyar Futua ya shirya jerin batutuwa domin bikin ranar yaki da shan miyagun kwayoyi wadda MDD ta ware. Daga cikin jerin abubuwan da za a aiwatar sun hada da gasar ka-ci-ci a tsakanin makarantun sakandare da kuma shirya taro tsakanin masu ruwa da tsaki domin lalubo bakin zaren wasu daga cikin matsalolin da ofishin hukumar na shirya ke fuskanta da lakca, domin bikin yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta wannan shekarar a shiyyar.