Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) reshen Kano ta kama mutane 49 a wani samamen kwana biyu da ta kai a faɗin jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na NDLEA, Sadiq Muhammad Maigatari, ya ce samamen ya gudana ne a ranakun 7 da 8 ga watan Agusta.
- Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ɗan Bindiga, Abubakar Abba
- Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N820 Kan Kowace Lita
Sun ƙwato kayayyaki da suka haɗa da tabar wiwi, kwayar Pregabalin, diazepam, ruwan magani mai ɗauke da codeine, Rohypnol, “Suck and die,” da makamai.
Sun kai samamen ne a wuraren da ake harkar miyagun ƙwayoyi kamar Massallacin Idi, Fagge Plaza, Kofar Mata, Kofar Wambai, Kofar Dan’agundi, Makabartar Dan’agundi, Ladanai, Zage, da Tashar Rimi a kasuwar Rimi.
Haka kuma, samamen da aka kai a tashar Kano Line da Tashar Rami da ke Na’ibawa ya kai ga kama wasu mutane 15.
Maigatari ya ce tun bayan ɗaga matsayin ofishin NDLEA na Kano zuwa babban mataki, aikin yaƙi da miyagun ƙwayoyi ya ƙara samun nasara.
Shugaban NDLEA na Kano, A.I. Ahmad, ya bayyana cewa wannan samamen na daga cikin ƙoƙarin bankaɗo maɓoyar masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da kuma daƙile ayyukan masu safarar ƙwayoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp