Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama kwalaben maganin kodin (codeine) guda 162,351 daga cikin kwantena biyu a tashar ruwan Apapa da ke Legas.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
- An Kammala Zangon Farko Na Canton Fair Karo Na 136
- Da Ɗumi-ɗumi: APC Ta Lashe Zaɓen Ƙananan Hukumomin Kaduna
Babafemi ya ce, jami’an hukumar sun cafke kwayoyin ne a yayin wani binciken hadin gwiwa a kwantena biyu da jami’an hukumar kwastam ta Nijeriya (NCS) da sauran jami’an tsaro a ranar 15 ga watan Oktoba.
Ya ce, an kwato kwayoyi 7,200,000 na ‘Royal 225mg Tapentadol’ da ‘Carisoprodol’ da kudinsu ya haura Naira biliyan 3.6 a farashin kasuwa.
Kakakin ya kuma ce, an kama kwayoyin ne da aka yi jigilarsu daga Indiya zuwa tashar ruwa a Fatakwal, Onne, ta jihar Ribas a ranar Talata 15 ga Oktoba.
“Acikin kwantenonin biyu, an kama kwayoyin Tapentadol, Carisoprodol da Codeine da kudinsu ya haura fiye da Naira biliyan 7,” inji shi.