Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta samu nasarar kama mutum 984 a watan Janairun zuwa wannan watan da muke ciki.
Shugaban hukumar ta NDLEA, Mohammed Buba Marwa,ne ya bayyana cewa, dukkan wadanda aka Kaman suna da dangantaka da aikata laifukan da ke da alaka da miyagun kwayoyi.
Marwa ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Yola, lokacin da sabbin zababbun shugannin kungiyar ‘yanjarida suka kai masa ziyara a gidansa. Ya ce mutum miliyam 15 daga cikin mutum miliyan 200, a Nijeriya na shan kwaya.
Ya ce, ganin yadda yawan wadanda ke shan kwayoyin ke karu wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar yaki da shan miyagun kwayoyi, a matsayin wata babbar hanya da ake fatan ta kawo karshen wannan matsala ta shan miyagun kwayoyi a wannan kasa.
Kamar yadda ya ce, yanzu haka ana kara gina gidajen horas wa da gyara tarbiyya.
Sannan kuma sai ya bukaci hadin kan al’umma da kuma kafofin yada labarai da su bayar da cikakkiyar gudummowarsu wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.
Buba Marwa ya kuma taya wadanda suka kai masa ziyarar murna bisa nasarar da suka samu a zaben da kungiyar ‘yanjaridar ta gudanar, sannan kuma sai ya bukaci su ci gaba da bayar da gudummowar da suka saba wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.
Tun farko, a nasa jawabin, shugaban kungiyar ‘yanjarida na jihar, Kwamared Ishaka Dedan, ya yi alkawarin cewa, za su bayar da cikakkiyar gudummowarsu wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.