Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, a ranar Talata, ta kona kilo 304,436 da kuma lita 40,042 na haramtattun abubuwa kayan maye da aka kama daga sassan jihohin Legas da Ogun.
Da yake jawabi a wani takaitaccen biki inda aka lalata magungunan da aka kama a bainar jama’a a Badagry, jihar Legas, shugaban hukumar NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya ce, kona miyagun kwayoyin da aka kama a fili ya biyo bayan umarnin kotu ne.
- Ka Sallami Duk Wanda Ya Gaza Kokari A Gwamnatinka – El-Rufai Ga Tinubu
- Gwamnatin Katsina Ta Raba Wa Jami’an Tsaro Sabbin Motocin Yaki
Marwa, ya yi kira ga jama’a da su kara tallafawa hukumar NDLEA kan kokarin da take yi na dakile yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi a Nijeriya.
Ya kara da cewa, jami’an hukumar ta NDLEA da ke aiki a sassa daban-daban ne suka kama haramtattun kayayyakin a jihohin Legas da Ogun daga watan Janairun 2022 zuwa yau musamman a tashoshin jiragen ruwa na Legas, da filayen jiragen sama, da kan iyakokin kasa.