Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kone kayan maye wadanda nauyinsu ya kai ton 26,wanda shi ne irinsa na farko a Jihar.
Shugaban Hukumar Birgediya- Janar Buba Marwa, ne ya bayyana cewar adadin mai yawa ne idan aka yi la’akari da alakar shaye- shaye da ayyukan ta’addanci a Jihar.
- NDLEA Ta Kwace Kilo Giram 390 Na Muggan Kwayoyi
- Ranar Yaki Da Miyagun Kwayoyi: NDLEA Ta Gurfanar Da Mutum 501 A Adamawa
A taron wanda aka gudanar yau, Marwa wanda Mataimakiyar Kwamanda -Janar a fannin miyagun kwayoyi, Josephine Ruth Obi, da ta wakilta, ta bayyana cewar an kama mutane 400 a yayin kama kayen mayen inda aka gurfanar da 95 a kotu tare da yanke masu hukunci.
Ya ce taron kone miyagun kwayoyin muhimmi ne domin dakile zagayawar a cikin al’umma ballantana su cutar da su.
Kayan da aka kone sun hada da kilogiram 14, 561. 632 na tabar wiwi da kilogiram 2. 710. 253 na miyagun kwayoyi da giram 4 na hodar iblis da kilogiram 8 na kodin wadanda suka kama kilogiram 25, 457. 232.
A jawabinsa Kwamandan Hukumar na Jihar Sakkwato, Iro Adamu Muhammad, ya bayyana cewar kone miyagun kwayoyin bayan samun umarni daga kotu daya ne daga cikin kudurin Shugaban Hukumar, Janar- Marwa, da yake yi na yaki da miyagun kwayoyi a Nijeriya.