Kwamandan Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Zamfara, Mista Gabriel Adamu Eigege ya sanar da cewa, Hukumar ta kwace kwaya da nauyinta ya kai kilo 4,520 sannan kuma ta gurfanar da mutum 28 a gaban kotu kan zargin su da shaye-shaye.Â
A hirarsa da kafar yada labarai ta Daily Post a garin Gusau Kwamandan ya ce, Hukumar ta kuma cafke maza 30 da mata 29 dauke da sama da Lita tara ta Kodine, inda kuma a yanzu hukumar ke bibiyar Shari’u 70 a gaban kutuna daban-daban.
Ya ci gaba da cewa Hukumar ta samu wannan nasarar ce bayan samun bayanan sirri tare da kuma hadakar da ta yi da Ma’aikatar kula da harkokin mata da yara ta jihar domin yaki da kayan maye a jihar.
A cewarsa, Hukumar ta kuma samu nasarar dakile wasu hanyoyin turowa da sayar da kayan mayen a jihar.
A karshe, Mista Eigege ya yaba wa Gwamnatin jihar Zamfara bisa tallafin da take cigaba da bai wa Hukumar wajen ganin ta sauke nauyin da aka dora mata don gudanar da ayyukanta.