A yammacin yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin.
Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, kasar Sin na son hada kai tare da kasar Rasha, wajen inganta hadin gwiwarsu ta hanyar da ta dace.
Kasar Sin tana son ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Rasha kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu, da manyan batutuwan da suka shafi harkokin ikon mulkin kasa, da tsaro, da yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, da karfafa tattaunawa da yin hadin gwiwa a tsakanin manyan kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya kamar MDD, da kasashen BRICS da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da sa kaimi ga bunkasuwar tsarin kasa da kasa da tafiyar da harkokin duniya bisa tsari na gaskiya da adalci.
A nasa jawabin, shugaba Putin ya bayhana cewa, kasar Rasha na goyon bayan shawarar kasar Sin kan tsaron kasa da kasa, kuma tana adawa da duk wani yunkuri na neman tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da batun Xinjiang, da Hong Kong da kuma yankin Taiwan.
Kasar Rasha na son karfafa hadin gwiwar bangarori daban-daban tare da kasar Sin, da yin kokarin da ya dace don bunkasa duniya mai kunshe da kowa, da kafa tsarin kasa da kasa mai adalci da ma’ana.
Haka kuma, shugabannin kasashen biyu, sun yi musayar ra’ ayi kan batun kasar Ukraine. Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana ci gaba da tafiya ne kan batun da ya shafi tarihi da kuma cancanta game da batun Ukraine, da yanke hukunci mai zaman kansa, da sa kaimi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsarin tattalin arzikin duniya.
Don haka, ya kamata dukkan bangarori su matsa kaimi wajen warware rikicin kasar Ukarine bisa gaskiya. Kasar Sin tana son ci gaba da taka rawar da ta dace a wannan fanni.(Ibrahim)