Hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO), ta bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na daliban da suka zana jarabawar kammala sakandare ta 2022 ne suka samu kyakkyawan sakamako.
Magatakarda kuma babban jami’in hukumar NECO, Farfesa Dantani Wushishi, wanda ya sanar da sakamakon jarabawar a hedkwatarta da ke Minna a ranar Alhamis, ya ce dalibai kashi 70 ne suka samu nasara a fannin lissafi da turanci.
- Shirin Twitter Space Na LEADERSHIP Hausa: Yadda ‘Yan Nijeriya Za Su Kauce Wa Komawa ‘Yar Gidan Jiya A Zaben 2023
- Bazan Daukaka Kara Ba, Na Amince Da Hukuncin Kotu Akan Mazabar Yobe Ta Arewa —Lawan
A cewarsa, masu ruwa da tsaki da dama sun amince da sakamakon jarabawar da aka yi a baya.
Mista Wushishi ya ce an fitar da sakamakon ne kwanaki 45 bayan kammala jarrabawar.
Ya ce adadin wadanda suka yi rajistar jarrabawar sun kai 1,209,703, maza 636,327, wanda ke wakiltar kashi 52.60 cikin 100 da mata 573,376, wanda ya nuna kashi 47.39 cikin 100.
Magatakardan ya ce dalibai 1,198,412, da maza 630,180 da ke wakiltar kashi 52.58 cikin 100 da mata 568,232 da ke wakiltar kashi 47.41 bisa 100 na dalibai a zahiri ne suka zana jarrabawar.