Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa Ta Jihar Neja, NSEMA, ta ce sama da mutane 410 ne suka mutu a wasu Ibtila’i da suka faru a jihar daga shekarar 2024 zuwa yau. Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Abdullahi Arah ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Minna, jiya.
Arah, ya ce duk da kalubale iri-iri da aka samu a wannan lokacin, ma’aikatan suna yin iyaka kokarinsu wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan NSEMA yadda ya kamata ta hanyar halartar abubuwan gaggawa daban-daban a fadin jihar.
- Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 1,191, Sun Ceto 543 Cikin Watanni Uku
- Ɗan Wasan Liverpool, Diogo Jota, Ya Mutu A Hatsarin Mota
A cewarsa, Ibtilala’i na farko da aka samu a 2024 shi ne fashewar tankar mai a Agaie, shalkwatar Karamar Hukumar Agaie wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 60, mutane takwas suka jikkata.
Babban daraktan ya bayyana cewa fashewar tankar mai ta Dikko wacce ta afku a ranar 18 ga watan Janairu, ta yi sanadin mutuwar mutum sama da 80, inda ya kara da cewa a tsawon wannan lokaci hukumar na hadin gwiwa da ma’aikatan lafiya tare da tura tawagar gaggawa domin shawo kan lamarin.
Akan tashin bam din da aka samu a Sabon Pegi da ke Karamar Hukumar Mariga, ya ce mutane biyu ne kawai suka mutu, yayin da gidaje da dama suka ruguje. Gwamnati ta bayar da kayan agaji da kudade ga wadanda abin ya shafa. “Na baya-bayan nan shi ne bala’in ambaliyar ruwa na Mokwa wanda ya raba dubban mutane da gidajensu, yayin da mutum 270 suka rasa rayukansu.
Hukumar ta NSEMA ta jagoranci gudanar da aikin, tare da tattara kayan aiki gami da tura kungiyoyin bayar da agajin gaggawa tare da hadin gwiwar hukumomin kananan hukumomi.’ Arah, ya bayyana cewa, kafin lokacin damina, hukumar ta NSEMA ta kaddamar da shirin wayar da kan jama’a game da ambaliyar ruwa a duk shekara a matsayin gangamin gargadin farko a ma’aikatun masarautu takwas, da nufin kara wayar da kan jama’a.
“NSEMA ta kuma bayar da agaji ga wadanda gobarar gidaje da kasuwanci ta shafa a sassan jihar”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp