Babban jami’in yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te, ya gabatar da jawabi a ranar Alhamis 10 ga watan nan, inda ya sake bayyana ra’ayin cewa wai bangarori biyu na gabar tekun Taiwan ba su da alaka da juna, da sabon ra’ayin kasancewar kasashe biyu, wanda hakan ya kasance karya ta neman ware yankin Taiwan daga babban yankin Sin, da zummar yayata ra’ayin kawo baraka, da zuga wutar yin fito-na-fito tsakaninsu. To sai dai kuma ikirarin nasa ba zai sauya ainihin gaskiya ba, wato yankin Taiwan wani sashi ne na kasar Sin.
“Sanawar Alkahira” da aka fitar a shekarar 1943, da “Sanarwar Potsdam” da aka sanar a shekarar 1945, dukkansu na tabbatar da cewa, Japan ta mayar wa kasar Sin yankin Taiwan da ta mamaye. Kuma hakan ya kasance muhimmin tushe na wanzar da doka da oda bayan Yakin Duniya na biyu, wanda kuma ya aza tubali a bangaren kare doka, don tabbatar da cewa yankin Taiwan ya kasance sashin kasar Sin da ba za a iya ware shi ba.
- Majalisar Tarayya Ta Samar Da Naira Biliyan 24 Domin Gyara Filin Jiragen Sama Na Kebbi Da Nasarawa
- MDD Ta Zartas Da Kudurin Kafa Yanayi Maras Shinge Ga Masu Bukata Ta Musamman
Yau shekaru 53 da suka gabata, a gun babban taron MDD karo na 26, an zartas da kuduri mai lamba 2,758, bisa kuri’un amincewa mafiya rinjaye, don mayar da ikon kasar Sin a majalisar, inda aka amince da cewa, wakilin gwamnatin babban yankin Sin kadai ne ke iya wakiltar kasar Sin a majalisar, kana an kori wakilin yankin Taiwan daga majalisar da sauran hukumomin MDD masu nasaba.
A cikin rabin karnin da ya gabata, majalisar da sauran hukumomin MDD, da kungiyoyin kasa da kasa, sun nace ga wannan kuduri ba tare da tangarda ba. Sin ta kuma kulla dangantakar diplomasiyya tsakaninta da sauran kasashe 183 bisa ka’idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Abin da ya alamta cewa, nacewa ga wannan ka’ida, matsaya ce daya tak a duniya baki daya, wadda ba wanda zai iya canja shi ta.
Makomar yankin Taiwan na dogaro da dinkewar kasar Sin, kuma farfadowar al’ummar Sinawa na amfanar al’ummun yankin Taiwan. A daya hannu, yunkurin masu neman kawo baraka kamar yadda Lai Ching-te yake yi za su ci tura. Dinkewar kasar Sin sha’ani ne da ba shakka zai tabbata, kuma ba wanda zai iya hana aukuwarsa. (Amina Xu)