Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai ya bayyana cewar, a matsayinsa na daya daga cikin mutum 37 da suka kafa jam’iyyar APC don haka yana daukar jam’iyyar a matsayin daya ce daga cikin ‘ya’yan da ya haifa a cikinsa.
Gwamnan wanda ke magana a shirin tsaiye da aka yada a dukkanin gidajen rediyon da suke jihar Kaduna a daren ranar Laraba, ya karyata jita-jitan da ke yawo na cewa shi din na yunkurin ficewa daga cikin jam’iyyar APC domin shiga wata jam’iyyar ta daban bisa zabin abokin takara.
El-Rufai ya sha alwashin cewa zai ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar APC har zuwa karshen rayuwarsa don haka ya ce mutuwa ce kawai za ta rabashi da APC, “Duk ranar da na fita a APC to daga wannan lokacin na bar siyasa ne gaba daya.”
Gwamnan ya ce wannan ba shine karo na farko da masu yada jita-jita a kansa ke yi ba, “da sun ce wai ina son na zama Shugaban kasa, suka dawo suka ce wai ina son na zama mataimakin dan takarar shugaban kasa, yanzu kuma sun dawo batun darakta Janar na yakin neman zabe”.
El-Rufai ya jaddada cewar Muhammad Sani Abdullahi, tsohon kwamishinan kasace da tsare-tsaren tattalin arzikin shine har yanzu dan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya, ya karyata batun wai shi din yana shirin maye gurbinsa.