Wani tsohon babban jami’in kudi, CFO na kamfanin Samar da man fetur na Najeriya, NNPCL, Umar Isa-Ajiya, ya musanta zargin cewa ta karfin tsiya jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC suka kama shi ranar Litinin da ta gabata, bisa zargin zamba.
Acikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, tsohon shugaban sashin kudin na kamfanin na NNPC, ya ce sabanin rahotanni dake kara-kaina, shi da kansa ya mika kansa ga hukumar, kuma babu wani lokaci da aka kama shi dangane da zargin karkatar da dala biliyan 7.2 na hada-hadar kasuwanci a matatar mai na Warri da Fatakwal.
- Nazarin CGTN: Neman Kashe Kaso 5 Na GDP Kan Tsaro Ya Nuna Rashin Dabara Na NATO
- Shugabannin Sin Da Mozamqiue Sun Mikawa Juna Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya
“Babu wanda ya kama ni kan zargin badakalar dala biliyan 7.2 dangane a matatar mai, na mika kaina babu tilastwa domin amsa tambayoyi ga hukumar EFCC, daga nan kuma na koma gida, sabanin yadda labarai ke yawo cewa an kama ni bisa zargin zamba” inji shi.
“Na yi aiki a kamfanin NNPC kuma na tafi da mutuncina, babu wanda ya zarge ni da wata zamba a tsawon zamana a Kamfanin, mutanen da ke yada wannan labarin na karya na kamawa da tsare ni kawai suna haka ne domin son su bata min suna.”
Mista Ajiya ya ce a shirye yake a kowanne lokaci don kare martabarsa da kuma tsawon shekaru da ya yi a hukumar ta NNPC, inda ya ce, “Ina kasar nan kuma a kowacce rana da kuma duk lokacin da EFCC ta bukaci na bayyana a gabansu zan zo”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp