Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro, samar da ingantaccen ilimi a kasar Nijeriya idan ya zama shugaban kasa.
Tsohon ministan tsaro kuma gwamnan jihar Kano, ya kuma ce zai bullo da kyawawan manufofin tattalin arziki da za su ciyar da kasar gaba.
Kwankwaso ya yi wannan alkawarin ne a ranar Litinin yayin da yake gabatar da jawabi a cibiyar ‘yan goro dake Calabar, a wata ganawa da wakilan jam’iyyar NNPP a Calabar.
Ya bayyana cewa, in ya lashe zaben, rashin tsaro da ya addabi al’ummar kasar nan a ‘yan kwanakin nan, zai zama tarihi da yardar Allah.
Ya ba da tabbacin samar da ingantaccen ilimi da ingantattun tsare-tsare na tattalin arziki da za su taimaka wajen juya arzikin kasa, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya na gida da na kasashen waje da su hada kai wajen zaben sa a matsayin shugaban kasa.