• English
  • Business News
Friday, October 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya A Shekara 65: Kwan-gaba Kwan-baya A Sha’anin Tsaro Da Siyasa Da Zamantakewa

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
1 hour ago
in Manyan Labarai
0
Nijeriya A Shekara 65: Kwan-gaba Kwan-baya A Sha’anin Tsaro Da Siyasa Da Zamantakewa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tarihi ya tabbatar da cewar a ranar 1 ga Oktoba 1960 aka sauke tutar Birtaniya a birnin Lagas, aka daga sabuwar tutar Nijeriya a matsayin ranar da ta kawo karshen mulkin mallaka tare da bude sabon babin tarihin kasar wato babin ‘yanci, da ‘yan Nijeriya suka jima suna fata.

A yau Nijeriya na murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai daga Turawan Birtaniya da suka yi wa kasar mulkin mallaka a tsayin shekaru. Wannan rana ta musamman ba wai ranar biki ce kawai ba, rana ce da al’ummar kasa ke waiwayen baya, suna nazarin nasarori, matsaloli da kalubalen da suka biyo bayan wannan dogon zango.

  • Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
  • Dubban Matasan Kano Sun Yi Zanga-zangar Lumana Domin Goyon Bayan CP AI Bakori

Ranar ‘yancin kai muhimmiyar rana ce da Tarayyar Nijeriya ta yi bankwana da mulkin bauta, rana ce da ‘yan kasa suka yi bankwana da mulkin mallaka, mulkin kama- karya kuma mulkin danniiya da zalunci wadda rana ce mai cike da dimbin tarihi.

Wannan ranar, rana ce ta tarihin kyakkyawar makoma, tarihin da ya kunshi burin ganin Nijeriya ta zama kasa mai cikakken iko, cike da alfahari a tsakanin sauran al’ummomin duniya.

Sai dai shekaru 65 da samun ‘yancin kai ba karamin lokaci ba ne, doguwar tafiya ce da ya kamata ta cika da gagarumin ci-gaba, amma tambayar da ke yawan tasowa ita ce; Shekaru 65 na ‘yanci, ci- gaba ne ko koma baya? Haske ne ko duhu? Dadi ne ko akasin haka?

Labarai Masu Nasaba

Ina Aka Kwana Batun Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Dazukan Jihar Katsina?

Dubban Matasan Kano Sun Yi Zanga-zangar Lumana Domin Goyon Bayan CP AI Bakori

A cikin shekarun 1940s zuwa 1950s, aka fara jin motsin neman ‘yanci daga manyan jam’iyyun siyasa kamar su NCNC a karkashin jagorancin Nnamdi Azikiwe, NPC a karkashin Sa Ahmadu Bello da kuma AG a karkashin Cif Obafemi Awolowo.

Bayan tattaunawar tsayin lokaci tare da shawarwari, Nijeriya ta samu damar gudanar da zaben farko a 1959 wanda ya bude kofar samun ‘yancin kai a inda Firayim Minista Sa Abubakar Tafawa Balewa ya zama shugaban gwamnati na farko, yayin da Dakta Nnamdi Azikiwe ya zama Gwamna Janar na kasa.

Masana tarihi da masu fashin bakin lamurran siyasa a Nijeriya na da ra’ayin mulkin kai ya haifar da alfanu mai dimbin yawa da kuma kalubale da dama ta fuskoki da bangarori da dama.

A yayin da ake murnar kafuwar mulkin dimokuradiyya na farko a karkashin jagorancin Firayim Minista Tafawa Balewa ba da jimawa ba, kalubalen kabilanci da rashin amincewa da juna ya jefa kasar a cikin rikici tare da kifar da gwamnati wanda hakan ya haifar da juyin mulkin farko a 1966 wanda ya bude sabon babin mulkin soja tare da mayar da kasar baya.

Tarihin siyasar Nijeriya ya zama kuma ya kasance tamkar kwan- gaba kwan- baya domin kuwa a bayyane yake cewar bayan juyin mulki an fada a kazamin yakin basasa a 1967–1970 wanda ya girgiza kasar bakidaya a tsayin lokaci.

Mulkin Nijeriya ya ci- gaba da tafiya a karkashin mulkin soja a tsawon shekaru kafin fafutukar da jajirtattun ‘yan kasa masu kishi suka yi wajen sake dawowa da kasar nan a saman mulkin dimokuradiyya a 1999.

Daga lokacin zuwa yau a shekaru 26 na mulkin farar hula, tsarin mulkin dimokuradiyya bai tsira daga raunin shugabanci, durkushewar masana’ntu da kuma matsalar zabe mai cike da murdiya da rikice- rikice ba.

Haka ma Nijeriya ta ginu ta kuma rayu a cike da matsalolin rikice- rikicen addini, kabilanci da rikicin makiyaya da manoma da cin hanci da rashawa wanda duk da kafa hukumomin EFCC da ICPC al’amarin ta’azzara ya yi maimakon raguwa.

A yau, mulkin dimokuradiyya ya zama ya kuma kasance fagen gwagwarmaya a tsakanin manyan jam’iyyun APC, PDP, LP da NNPP da kuma sabuwar jam’iyyar hadaka ta ADC da ta bayyana a fafutukar zaben 2027 wanda ya riga ya dauki hankalin al’ummar ciki da wajen kasa.

Duk da tsayuwar mulkin dimokuradiyya, Nijeriya na fuskantar babban kalubalen tabbatar da gaskiya da ingantaccen shugabanci wanda zai amfanar da talakawa ba shugabanni kadai ba wadanda talakawa ke kuka da kokawa da jagorancin su.

A tsayin shekaru 65 na samun ‘yancin kai, baya ga yakin basasa, matsalar tsaro da ta yadu a shekarun da suka biyo baya gagarumar matsala ce mai zaman kan ta wadda hukumomin tsaro suka kasa takawa burki.

Hasalima Nijeriya na ci-gaba da iyo da ninkaya a kogin kisan gilla da ya zama tamkar ruwan dare tun daga kan gagarumar matsalar Boko- Haram da ta ’yan ta’adda a Arewa- maso- Gabas da Arewa- maso- Yamma wanda shine babban kalubalen da ya fi kowanne tasiri ga rayuwar al’umma tun bayan samun ’yancin kai.

Rikicin Biafra ya bar zazzafan tarihi daga 1967 zuwa 1970, amma daga shekarar 2009 zuwa yau yakin Boko- Haram ya zama babbar annobar sha’anin tsaro da ya girgiza ya kuma raunana Nijeriya wanda ya kassara Arewa- maso- gabas da al’ummar ta tamkar kasar da babu gwamnati.

Yakin Boko- Haram wanda ya fara da tsattsaurar akidar addini daga baya ya koma lamarin da ya fi kama da kasuwancin rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, mayakan Boko- Haram sun tarwatsa dubban garuruwa a Borno, Yobe da Adamawa, sun kashe dubban daruruwan mutane, sun tilasta miliyoyin mutane tserewa daga gidajensu, sun kuma kona makarantu da asibitoci.

Baya ga matsalar Boko- Haram, kungiyar ISWAP ta sake kunno kai tare da kai munanan hare-hare kan sojoji da al’umma. Harin Gwoza, Rann, Damasak da Baga ya nuna yadda kungiyoyin ke da karfin kai hari tare da kwace makamai daga hannun dakarun gwamnati.

A Arewa- maso- Yamma kuwa, matsalar barayin daji da ke cin karensu ba babbaka ta dauki sabon salo ta yadda suke addabar jihohin Zamfara, Katsina, Sakkwato, Kaduna da Kebbi da dukkan karfin su ba tare da jami’an tsaro sun yi galaba kan su ba.

‘Yan ta’adda sun kafa sansanonin ta’addanci a dazuka inda suke gudanar da garkuwa da mutane tare da karbar kudin fansa. A sanadiyar gallazawarsu makarantu da dama sun rufe saboda hare- haren sace dalibai da malamai, sannan dubban mutane sun rasa rayukansu da gonakinsu.

Barayin dajin sun mayar da titunan kasar nan lahira kusa domin kuwa hanyoyin Kaduna– Abuja, Zamfara– Sakkwato da Katsina– Kano ko Birnin Kebbi- Neja- Abuja, fasinjoji na tafiya cike da fargabar farautar rayukan su da ’yan bindiga ke yi.

A kauyuka kuwa, rayuwa ta zama cike da hadari ta yadda jama’a ke cike da bala’in yadda ‘yan ta’adda ke tilasta masu biyan haraji kafin su ba su damar zuwa gona domin noma albarkatun gona ko girbe su ko ma zuwa kasuwa tamkar kasar da barayin daji ke da iko a kan kowa.

A bayyane daga 2009 zuwa yau babu sahihan adadin kididdigar mutanen da suka bakunci lahira daga fara kisan kare dangi da Boko- Haram suka yi wa al’ummar Arewa- maso- Gabas da dimbin jama’ar da yunwa ta kashe a yankin domin masana harkokin tsaro na ganin adadin mutane 35, 000 da ake ambato da mayakan suka kashe da mutane sama da dubu 100, 000 da ake hasashen yunwa ta kashe sun zarce haka nesa ba kusa ba.

Bugu da kari barayin daji a Arewa- maso- Yamma sun ci karen su ba babbaka kuma suna ci-gaba da cin karen su ba babbaka tare da ikirarin sun fi karfin jami’an tsaro su yi galaba a kan su. A kan hakan ‘yan bindigar sun kashe dubban al’umma maza da mata, sun yi garkuwa da mutane ba adadi, sun kone garuruwa da amfanin gona fiye da kima tare da bugun gaban ci-gaba da gallazawa jama’a son ran su.

A dukkanin kashe- kasshen sun bar dubban rayuka cikin hasara da miliyoyin mutane da suka kauracewa gidajensu tare da zama ‘yan gudun hijira a cikin yanayin yunwa, tausay da kazanta.

A bangaren zamantakewa za a iya cewa tafiya ce mai cike da kalubale da nasarori. An samu ci- gaba wajen kafa makarantu, jami’o’i da cibiyoyin lafiya, amma matsalolin yajin aiki, karancin kayan aiki da rashin rikon amana sun raunana su.

Tattalin arzikin Nijeriya ya dogara ne da man fetur, duk da albarkatun kasa da ake da su jibge wadanda ake haka ba bisa ka’ida ba, amma mafi yawan jama’a na fama da talauci. Rashin daidaiton rarraba arziki da rashin aikin yi ya jefa matasa cikin rudani, wanda hakan ke sa da dama daga ciki shiga sabgar ta’addanci da safarar miyagun kwayoyi.

Ko tababa babu shekaru 65 bayan samun ’yanci daga turawan Birtaniya, shekaru ne da Nijeriya ta yi cike da darussa, shekarun nasarori da alfahari kamar yadda a bayyane akwai lokutan koma baya da jajantawa juna.

A bangaren siyasa kai tsaye za iya cewa an samu gagarumin ci- gaba wajen dorewar mulkin dimokuradiyya a tsayin shekaru 26 ba tare da katsalandan din soja ba wanda hakan ke nuna tsayuwar mulkin dimokuradiyya, sai dai raunin shugabanci da cin hanci suna ci- gaba da zama barazana.

Bikin cikar shekaru 65 da samun ’yancin kai bai kamata ya tsaya kan shagali da murna kawai ba. Yana da matukar muhimmanci a koma baya a duba tarihi, a fahimci kura-kurai da kuma darussa. Nijeriya na bukatar shugabanci nagari, ingantaccen tsaro da tsarin mulkin gaskiya da adalci domin tabbatar da cewa shekaru masu zuwa za su kasance kwan gaba, ba kwan baya ba.

Samun ‘yancin kai da bankwana da mulkin mallaka, bai sa Nijeriya ta yi bankwana da talauci ba domin kuwa rahotanni sun nuna a halin yanzu adadin mutane miliyan 129 suna rayuwa a kasa da matakin talauci na kasa sosai, wato kusan kashi 60% na yawan al’umma.

Haka ma wani binciken ya nuna kusan ‘yan Nijeriya mutane miliyan 133 suna rayuwa ne a cikin matsanancin talauci wanda hakan kadai ya nuna irin mummunan yanayin da al’ummar kasa ke ciki.

A ra’ayin wani dattijo Mahadi Adamu bai yi kasa a guiwa ba wajen cewa “Tun lokacin da muka samu ‘yanci a 1960 har zuwa yau, gwamnati ta kashe makudan kudade wajen gina matatun mai, amma babu daya da ke aiki. Dukkanmu muna dogaro da shigowa da man da ake tacewa a kasashen waje. Wannan babban abin kunya ne ga kasa mai shekaru 65 da cin gashin kanta,” n ji shi cikin bakn ciki.

Dattijon ya kuma yi nuni da cewa abin takaici ne cewa matatar mai ta Dangote, wadda dan kasa mai kishin kasa ya gina da kudinsa wadda ke nuna ci-gaba ga al’ummar Nijeriya, amma maimakon a tallafa mata, a na zargin gwamnati da wasu manyan kamfanonin mai na cikin gida da na waje da yi mata zagon kasa.

Sahabi Abubakar dalibi ne a jami’ar Usmanu Danfodoyo da ke Sakkwato ya kuma bayyana ra’ayinsa da samun ‘yanci da cewar “abin farin ciki ne a ce Nijeriya ta kai shekaru 65 da samun ‘yanci, amma a gaskiya har yanzu ba mu mori wannan ‘yancin yadda ya kamata ba. Tabarbarewar ilimi, yawaitar talauci, karuwar rashin tsaro, da rashin aikin yi sun sa matasa karaya da kasar nan.”

Ita kuwa wata tsohuwa Hafsatu Lawal ga abin da ta ce “Tun lokacin ‘yanci, mun ga abubuwa da dama sun faru. Akwai ci- gaba a fannoni da dama amma dai gwamnati ta kasa kwarai wajen kasa samar da wutar lantarki, kasa magance matsalar tsaro, kasa farfado da matatun mai da bunkasa kiyon lafiya da rashin aikin yi da sauransu.”

Idan aka yi amfani da damar arzikin kasa da nagartattun mutane da ke kasar nan ke da, babu shakka Nijeriya na iya zama babbar jagora a nahiyar Afirka. Amma idan aka ci gaba da yin sakaci da tsaro da shugabanci, tarihi zai ci- gaba da maimaita kansa wanda hakan shi ne mafi munin kwan baya.

Masana na ganin makomar Nijeriya ta dogara kan samar da tsaro mai dorewa, fadada tattalin arziki ta hanyar noma da masana’antu, inganta sha’anin ilimi da lafiya, karfafa bin doka da yaki da rashawa tare da inganta hadin kan kasa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Nijeriya
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ina Aka Kwana Batun Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Dazukan Jihar Katsina?

Next Post

Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

Related

Katsina Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Mahaddata Alƙur’ani – Gwamna Radda
Manyan Labarai

Ina Aka Kwana Batun Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Dazukan Jihar Katsina?

2 hours ago
Dubban Matasan Kano Sun Yi Zanga-zangar Lumana Domin Goyon Bayan CP AI Bakori
Manyan Labarai

Dubban Matasan Kano Sun Yi Zanga-zangar Lumana Domin Goyon Bayan CP AI Bakori

13 hours ago
Wata Mata Ta Banka Wa Kanta Wuta Har Lahira A Bauchi
Manyan Labarai

Wata Mata Ta Banka Wa Kanta Wuta Har Lahira A Bauchi

17 hours ago
PENGASSAN Ta Musanta Janyewa Daga Yajin Aiki, Ta Gargaɗi Dangote
Manyan Labarai

PENGASSAN Ta Musanta Janyewa Daga Yajin Aiki, Ta Gargaɗi Dangote

19 hours ago
Shettima Ya Dawo Abuja Bayan Ziyarar UNGA Da Jamus
Manyan Labarai

Shettima Ya Dawo Abuja Bayan Ziyarar UNGA Da Jamus

22 hours ago
‘Yansanda Sun Kama Barayi 15, Sun Kwato Motocin Sata 20 A Kano
Manyan Labarai

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kama Ɓarayi A Jihar Neja

23 hours ago
Next Post
Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

LABARAI MASU NASABA

Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

October 3, 2025
Nijeriya A Shekara 65: Kwan-gaba Kwan-baya A Sha’anin Tsaro Da Siyasa Da Zamantakewa

Nijeriya A Shekara 65: Kwan-gaba Kwan-baya A Sha’anin Tsaro Da Siyasa Da Zamantakewa

October 3, 2025
Katsina Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Mahaddata Alƙur’ani – Gwamna Radda

Ina Aka Kwana Batun Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Dazukan Jihar Katsina?

October 3, 2025
Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin

Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin

October 2, 2025
Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Tallafawa Ɗalibai 16,756 Da Naira Miliyan 592

Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Tallafawa Ɗalibai 16,756 Da Naira Miliyan 592

October 2, 2025
Gwamna Lawal Ya Gwangwaje Kamfanin Sufurin Mota Na Zamfara Da Motoci 50 

Gwamna Lawal Ya Gwangwaje Kamfanin Sufurin Mota Na Zamfara Da Motoci 50 

October 2, 2025
Balaguron Fasinjoji Ta Jirgin Kasa A Kasar Sin Ya Kai Matsayi Mafi Girma A Bikin Ranar Kafuwar PRC

Balaguron Fasinjoji Ta Jirgin Kasa A Kasar Sin Ya Kai Matsayi Mafi Girma A Bikin Ranar Kafuwar PRC

October 2, 2025
Dubban Matasan Kano Sun Yi Zanga-zangar Lumana Domin Goyon Bayan CP AI Bakori

Dubban Matasan Kano Sun Yi Zanga-zangar Lumana Domin Goyon Bayan CP AI Bakori

October 2, 2025
Xi Ya Taya Jami’ar Tianjin Murnar Cika Shekaru 130 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Jami’ar Tianjin Murnar Cika Shekaru 130 Da Kafuwa

October 2, 2025
‘Yansanda Sun Ƙwato Muggan Ƙwayoyi Na Naira Miliyan 120 A Kano

‘Yansanda Sun Ƙwato Muggan Ƙwayoyi Na Naira Miliyan 120 A Kano

October 2, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.