Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce Nijeriya ba ta da wata alaƙa da gwajin makamin nukiliya kuma tana goyon bayan haramcin hakan ɗari bisa ɗari.
Shettima ya faɗi haka ne lokacin da ya gana da wata tawaga daga hukumar hana gwajin makaman nukiliya (CTBTO) ƙarƙashin jagorancin sakataren hukumar, Dr Robert Floyd, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Karfafa Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Kan Tinkarar Sauyin Yanayi
- Da Ɗumi-Ɗumi: Osimhen Ya Amince Da Komawa Galatasaray Na Dindindin
Ya ce kamar sauran ƙasashen Afirka, Nljeriya na fama da matsalolin rayuwa da tattalin arziƙi, irin su talauci da sauyin yanayi, wanda ke barazana ga rayuwar al’umma.
Saboda haka, a cewarsa, ba makaman nukiliya Nijeriya ke buƙata ba, sai mafita kan waɗannan matsaloli.
A nasa jawabi, Dr Robert Floyd ya jinjina wa Nijeriya kan yadda ta ke goyon bayan shirin hana gwajin makaman nukiliya.
Haka kuma ya yaba da irin rawar da shugaba Bola Tinubu ke takawa wajen tallafa wa zaman lafiya ta hanyar hana yaɗuwar irin waɗannan makamai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp