Bayan kammala wasannin Yammacin Afirika, Nijeriya ta samu matsayi na daya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle da aka gudanar a kasar Ghana.
Nijeriya ce ta zo kan gaba bayan kammala gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a gasar Afirka ta 2023 a ranar Juma’a.
- Tarihin Masarautar Zazzau Da Sarakunanta (1)
- Abincin Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Ci Da Wanda Bai Kamata Ba
Nijeriya ta lashe manyan kyaututtuka a gasar inda ta samu lambobin yabo 21 da suka hada da zinari 11, azurfa shida da tagulla hudu.
Wannan dai shi ne karo na hudu da kasar ta taka rawar gani a tarihin wasannin na kasashen Afirka ta Yamma, manyan ‘yan wasa irinsu Tobi Amusan, Ese Brume da Chukwuebuka Enekwechi, sun ci gaba da rike kambunsu a tseren mita 100 na mata da na maza, bi da bi.
A tseren mita 400 na maza, Chidi Okezie ya kafa tarihi a matsayin dan Nijeriya na farko da ya lashe zinare a gasar cikin shekaru 37, irin su Ruth Usoro, Pamela Obiageri, da Amaechi Chinecherem Nnamdi, suma sun samu zinari a wasannin da suka fafata daban-daban.