Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Idris Isah Jere ya jagoranci tawagar Nijeriya wajen tattauna wasu batutuwa da suka shafi shige da fice a tsakanin Nijeriya da Birtaniya a Abuja, ranar Laraba.
Shugaban hukumar, ya ce, kulla yarjejeniyar hadin guiwa da kasar Birtaniya kan shige da fice ya haifar da ad mai ido.
A cewarsa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu ta taimaka wajen rage kwararan bakin haure daga Nijeriya zuwa Birtaniya ba bisa ka’ida ba.
- Kawu Sumaila Ya Gargadi Tinubu Kan Yi Wa Majalisa Katsa-Landan
- ‘Yansanda Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato Bindigogi A Zamfara
A cewarsa “Rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta bakin haure ba wai kawai ta samar da alakar da ke tsakanin kasashen ba ne, har ma da bude hanyar ci gaba da yin hadin gwiwa don kare ‘yan kasashen biyu, da tunkarar barazanar da ake fuskanta a fannin hijira.
“Zan bayar da shawarar cewar yana da kyau a mutunta mutanen da aka dawo da su daga ci-rani don martaba su a matsayinsu na ‘yan Adam.”
Jere ya ja hankali kan yadda ake samun tsaikon samun biza ga ‘yan Nijeriya da ke son zuwa Birtaniya, wanda ya ce hukumar na tattaunawa da mahukuntan Birtaniya don shawo kan matsalar.
Sai dai ya ja hankalin mutane kan cewar yana da kyau suke shirya tafiye-tafiyensu a hukumance ga ma’aikatan gwamnati.
Kazalika, ya yaba wa Birtaniya kan shirinta na dakile safarar mutane a tsakanin Nijeriya da Nijar, lamarin da ya ce ya haifar da da mai ido.
“Shirin ya taimaka wa Nijeriya wajen hada kai sosai da Jamhuriyar Nijar wajen magance matsalar safarar bakin haure,” in ji shi.
Ya ce hukumar za ta kara kaimi wajen ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda suka dace.