Nijeriya da kasar Brazil sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a bangaren kasuwanci ta ‘Green Imperative Project’ (GIP) na dala biliyan 1.1 domin bunkasa harkokin noma da zuba hannun jari ga kamfanoni masu zaman kansu a Nijeriya.
Wannnan na cikin matakan kariya kan wadata kasa da abinci.
Shirin GIP, shiri ne kan aikin noma mafi girma a Afirka wanda ke ba da fifiko ga ci gaban noma mai dorewa, yana da nufin habaka yanayin tsari don samar da abinci a Nijeriya cikin inganci.
- Hauhawar Farashi A Nijeriya Ta Ragu Zuwa 23.18 Cikin 100 A Fabrairu — NBS
- Azumi Ya Dara Wa Sauran Ibadu
A shekarar 2018 ne aka fara rattaba hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 1.1 na GIP 1, yayin da kashi na 2 na shirin dala biliyan 4.3 da kuma JBS na dala biliyan 2.5 aka sanya hannu a Brazil a ziyarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai kasar a bara.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya misalta sanya hannu kan shirin farko na kasuwancin GIP 1 a wani mataki na gwamnatin Tinubu na wadata kasa da abinci.
Da yake jawabi yayin rattaba hannu a rukunin shirin kasuwanci GIP 1 a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Shettima ya ce shirin GIP zai bude wasu damarmakin masu tarin yawa da za su kai ga bude kofofin ci gaban tattalin arzikin kasa da inganta kwarin gwiwa ga masu zuba hannun jari a Nijeriya.
Ya ce, “Yayin da wannan gwamnatin ke kan kokarin magance kalubalen samar da abinci da muke fuskanta tare da maida hankali kan ajandar guda 8 na Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya zama wajibi mu hada hannu tare da yin amfani da shirye-shiryen da ake da su kamar su GIP domin ci gaba da manufofinsu, yin amfani da dabaru da hikimomin bunkasa tattalin arzikinmu da kuma kara kwarin gwiwar masu zuba jari.”
Shettima ya lura cewa, yayin da GIP ya yi daidai da manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu, ya ce, shirin zai kyautata harkokin kananan manoma da sauran harkokin da suka shafi noma a fadin kasar nan.
Ya ce tabbas shirin zai taimaka wajen magance matsaloli da dama da manoma ke fama a Nijeriya, musamman kananan manoma da suke fuskatar matsalar fitar da amfani gona.
Bisa wannan nasarar sanya hannun da aka samu, mataimakin shugaban ya jinjina wa ministan noma, ministan kudi, ministan shari’a da ministan harkokin waje da sauran wadanda suka dafa har aka kai ga wannan matakin.
Shi kuma a bangarensa, Jakadar Brazil a Nijeriya, Carlos Garcete, ya ce babban abin alfahari ne ga Brazil ta hada kai da ‘Green Imperatibe Project (GIP), yana mai cewa a cikin shekaru bakwai da suka gabata, an yi shawarwari da gwamnatin Nijeriya da nufin samun kudaden da ake bukata daga bankuna masu zaman kansu da na raya kasa na yanki don gudanar da wannan gagarumin aiki, wanda ya kai kusan dala biliyan 1.1.
A madadin gwamnatin kasar Burazil, Mista Garcete ya jinjina wa Shugaban Tinubu bisa nasarar tabbatar da dogon muhawarar yiyuwar shirin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp