A ranar Alhamis ne ake kyautata zaton gwamnatin tarayya za ta rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da kasar Morocco kan aikin bututun iskar gas na Nijeriya mai nisan kilomita 7000.
Shugaban kamfanin Mai na Kasa, Mele Kyari ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai wa shugaban hukumar ECOWAS, Dakta Omar Touray ziyara a Abuja.
Ya ce da zarar an kammala aikin, zai samar da kusan 3bscfd na iskar gas a gabar tekun yammacin Afirka daga Nijeriya zuwa Kasar Benin, da Togo, da Ghana, da Cote d’Ivoire, da Laberiya, da Saliyo, da Guinea, da Guinea Bissau, da Gambia, da Senegal, da Mauritania sai Morocco.
Ya tabbatar da cewa, hadin gwiwar za ta kawo samun nasarar aikin, aikin zai samar da iskar gas ga kasashen yammacin Afirka zuwa Masarautar Morocco daga bisani kuma zuwa Turai.