Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sun jagoranci kulla yarjeniyoyi daban-daban tsakanin kasashen biyu a birnin Doha.
Kasashen biyu sun sanya hannu kan jarjeniyoyin da suka shafi harkokin ilimi da zuba jari da inganta rayuwar matasa da harkokin ma’adinai da harkokin yawon bude ido da wasanni.
- An Bude Taron Majalisar Wakilan Jama’Ar Kasar Sin A Beijing
- Labaran Karyar Cewa “Tattalin Arzikin Sin Na Dakushewa” Ba sa Tasiri A zukatan Jama’a
Gabanin bikin sanya hannu kan yarjeniyoyin a Fadar Shugaban Kasar Qatar, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa mai masaukin baki cewa a shirye gwamnatinsa ta ke ta yi maraba da masu zuba jari a kasar.
Ya yi nuni da sauye-sauyen da yake gudanarwa wadanda za su taimaka wajen bunkasa samun tagomashi a harkar zuba jari da kyautata al’adu.
“Babban jarinmu shi ne al’umarmu. karfinmu ya ta’allaka kan kwazon matasan Nijeriya. Suna da kuzari da basira da jajircewa. Za su kasance abokan hulda a masana’antun Qatar. Suna da ilimi da nagarta, kuma suna neman inganta kowane tsari da suka samu,” a cewar Shugaba Tinubu.
Tinubu ya jinjina wa gwamnatin Qatar bisa sauye-sauye da ci gaban da ta ke samu.
A nasa bangaren, Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya jaddada cewa a shirye kasarsa ta ke ta yi maraba da batun zuba jari.