Nijeriya na rasa kusan fam biliyan £1.5 a kowace shekara sakamakon matsalolin lafiya da tattalin arziki sakamakon yin bayan gida a bainar jama’a.
Cututtuka kamar gudawa da kwalara, wadanda ke tsananta saboda rashin tsaftar muhalli da gurbataccen ruwa, suna haifar da tsadar magani, raguwar aikin yi, da haifar da mutuwa.
- Kotu Ta Bada Belin Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Kan Naira Milyan 10 Kowanensu
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 49 A Yankuna 226 A Kano — SEMA
Domin magance wannan matsala, Gwamnatin Tarayya da UNICEF sun shirya taro a Jihar Legas don karfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu su taimaka wajen kawar da yin bayan gida a fili zuwa shekarar 2030.
Wannan taro ya yi daidai da manufofin ci gaban duniya (SDGs).
Misis Elizabeth Ugoh daga Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Tsafta ta ce duk da kokarin da ake yi, kananan hukumomi 126 ne kawai daga 774 suka samu nasarar kawar da yin bahaya a fili.
Ta yi kira da a kara sanya kudade, don inganta ababen more rayuwa, da goyon bayan kamfanoni masu zaman kansu don shawo kan wannan matsalar.
Dokta Jane Bevan daga UNICEF da Céline Lafoucrière sun bayyana bukatar kamfanoni masu zaman kansu su saka hannun jari kan matsalar yin bahaya da ayyukan tsafta.
Sun ce hakan na faruwa ne sakamakon akalla mutane miliyan 48 a Nijeriya ba su da bayan gida.
Sun nuna cewa dole ne kowa ya hada hannu, ciki har da kamfanoni, don inganta harkar tsafta, wanda kuma zai iya kawo riba ga harkar kasuwanci.
Ofishin Harkokin Kasuwancin na Jihar Legas, ya bayyana cewa saka jari a abin da ya shafi tsafta na iya haifar da riba mai yawa, inda ya ce bincike ya nuna za a samu ribar fam £5.50 kan kowane fam £1 da aka kashe.