ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Na Bukatar Dala Biliyan 10 Kowace Shekara Domin Samun Ingantacciyar Wutar Lantarki — Minista

by Yusuf Shuaibu
7 months ago
Lantarki

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Nijeriya na bukatar dala biliyan 10 a kowace shekara kafin kasar ta samu ingantacciyar wutar lantarki na tsawon shekara goma zuwa ashirin masu zuwa.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin kaddamar da tashar wutar lantarki ta Solar PV da ta kasance mai karfin 600kW da 3MW a makarantar horar da sojojin Nijeriya da ke Kaduna.

  • Adadin Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Aiki Da Lantarki Na Sin Ya Karu Da 47.6% A Shekara 
  • Majalisar Kano Ta Amince Da Dokar Wutar Lantarki Da Za Ta Raba Wa Jihohi 3 Wuta

Ya kara da cewa akwai matsalolin da aka fuskanta a baya, wanda dole ne a magance su domin wannan matakin zuba jari ya zama mai ma’ana.

ADVERTISEMENT

“Lamba ta daya ita ce, tsarin dokoki da manufofi, wanda wannan gwamnatin ta cimma ta hanyar sanya hannu kan kudirin dokar makamashi zuwa doka.”

“Wannan doka ta tabbatar da ingantawa da tsarin wutar lantarki, tana ba dukkan matakan gwamnati tarayya, jiha, da kananan hukumomi dama a hukumance da kuma taka muhimmiyar rawa a cikin fannin wutar lantarki don amfanin al’umma a matakan kasa.”

LABARAI MASU NASABA

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

“Wannan ya ba wasu jihohi fiye da goma sha daya ‘yancin kai, tare da karin wadanda ake sa ran za su biyo baya. Wadannan jihohin yanzu suna iya shiga cikin masana’antar wutar lantarki, daga samarwa har zuwa isarwa, rarraba, har ma da samar da mitoci.”

“Na biyu, dole ne mu magance rashin ingancin ababen more rayuwa, wanda ya taru a cikin shekaru 60 da suka wuce saboda rashin kula da rashin isasshen zuba jari don farfado da tsarin zamanantar da wutar lantarki.”

Ministan ya kuma jaddada bukatar cike gibin mita na sama da kashi 50 bisa dari, yana mai cewa shirin shugaban kasa yana nufin cimma wannan ta hanyar girka mita miliyan 18 a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Ya ce an kaddamar da wutar lantarki ta tashar Solar PV mai karfin 600kW da 3MW a makarantar horar da sojojin Nijeriya domin bai wa gwamnatin tarayya kwarin gwiwa wajen magance karancin wutar lantarki.

Daraktan gudanarwa na Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA), Abba Abubakar Aliyu, ya bayyana kaddamar da aikin hasken rana na 2.5MW a matsayin wata mafita ga Nijeriya wajen samun wutar lantarki ga makarantun ilimi.

Ya kara da cewa hukumar ba kawai tana kaddamar fara wani aiki ba ne, tana kuma lura da tasirin zamantakewa, bincike, da ci gaban mai dorewa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa
Labarai

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Next Post
Zargin Cin Zarafi: Gaskiyar Halin Da Ake Ciki A Gidan Yarin Goron Dutse

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.