Sam Nda-Isaiah, Shugaban da ya kafa Kamfanin LEADERSHIP, wanda aka fi sani da Uncle Sam, da yana raye zai zama ya cika shekaru 62 a duniya, a ranar 1 ga Mayu, 2024. Yayin da iyalansa, abokansa da kuma daukacin ma’aikatan LEADERSHIP ke alhinin rashinsa da kuma cika shekaru 62 da haihuwarsa, mun kawo wa masu karatunmu daya daga cikin sharhohin da ya yi a kan Nijeriya kamar yadda aka taba wallafawa a shafinsa mai suna “The Last Word” a watan Maris, 2009.
A makon da ya gabata, na kwarmata cewa, darajar Naira ta fadi cikin sauri zuwa N163 a kan dala daya. Na kuma tattauna hadarin da ke tattare da kasa mai dogaro da shigo da kayayyaki kamar Nijeriya. Amma kash! ina magana ne da shugabannin da ke nuna halin ko in kula. Kuma tabbas yanayin da ake ciki ya nuna hakan. Da safiyar Alhamis, abin ya koma N172 a kan dala daya; kuma, da yammacin ranar, dalar ta koma N175. A lokacin ne na rasa lalubo bakin zaren lissafi. Domin kuwa dala ta yi karanci a makon da ya gabata, da wuya a ci gaba da kare faduwar darajar Naira. A wasu wurare, sai ka je sannan za ka san asalin farashin dalar.
- Nijeriya Da Japan Sun Kulla Yarjejeniya Don Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Yankin Sahel
- Jihar Kaduna: Rikicin Bashi Da Rashin Sanin Tsarin Gudanar Da Mulki
Abin da hakan ke nufi shi ne, a makon da ya gabata, yawancin ‘yan kasuwar Nijeriya ba su yi kyakkyawan shiri ba. Wasu daga cikin wadanda suka dogara da shigo da kaya dole ta sa suka dakatar da ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci har sai sun fahimci yadda al’amura suke baro-baro a fili. Yayin da duk hakan yake faruwa, guguwar hauhawar farashin kayayyaki ta fara kadawa.
Za a dade ana jin jiki game da rikicin canjin kudaden waje. Amma matsalar ita ce, da alama babu haske bayan duhu kan lamarin. Wannan hanya, abin bakin ciki, tana kama da rami mai mugun zurfi. Wasu masu hasashe ma sun bayyana cewa darajar Naira za ta ruguje ta koma N200 a kan dala.
Har ila yau, akwai wani mummunan labarin ma. A makon da ya gabata ma, Shugaban Kasa Umaru ‘Yar’aduwa ya bayyana shirinsa na bunkasa tattalin arziki, wanda a fili yake abin ya yi kama da wani bala’i da ba za a taba mantawa da shi ba ga al’ummar Nijeriya. Daga karshe dai gwamnati ta amince da sadaukar da ikon tafiyar da tattalin arziki. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da iyaye da ubangidan masu son a mika ikon tafiyar da tattalin arziki ga ‘yan kasuwa da ke cikin manyan biranen Turai da Amurka ke jan baya ko kuma suke lalata ka’idojin da suka yi amanna da su na jari hujja. A makon da ‘Yar’Adua ya sanar da shirinsa na sadaukar da ikon tafiyar ta tattalin arziki ga ‘yan kasuwa, a makon ne kuma Gwamnatin Amurka ta mayar da Bankin Citibank ya dawo hannun kasa. Kafin wannan lokacin, sabuwar gwamnati a Amurka ta yi ishara da cewa, saboda tabarbarewar tattalin arzikinsu, yanzu gwamnati za ta rika sa hannu a kan wasu ka’idoji na kasuwanci da ake kafawa. Haka abin yake a tsakanin gwamnatocin Burtaniya, Faransa da galibin kasashen Turai.
Duk mai wayewa ya yarda cewa wannan ce kawai hanyar da za a bi a kai ga tudun mun tsira wannan lokacin. A yayin da ake cikin mawuyacin hali irin wannan, gwamnati ce kawai ke da ikon bayar da gagarumar gudunmawa a kan yunkurin da za a bukaci yi na neman mafita a kan mummunan halin da ake ciki. Yana da wuya a iya fahimtar daga ina Yar’Adua da mutanensa suka samo mafitarsu. Aiwatar da shawarar sadaukar da ikon tafiyar da tattalin arziki a daidai lokacin da darajar Naira ke karyewa da kuma koma bayan tattalin arziki sun nuna yadda gwamnatin Nijeriya ke da mugun nufi. Shugabanninmu sun tilasta mana kansu a kan shugabancinmu sannan suna ci gaba da azabtar da mu.
Shugaban ya yi imanin cewa masu zuba jari da yawa za su shigo da kudaden da suka tara da jibin goshinsu don gina matatun mai a cikin Nijeriya. Amma da gaske, mahaukacin mai zuba hannun hannun jari ne kawai zai iya kawo irin kudin da ake bukata don gina matatar mai a kasar nan tare da samar wa kansa da wutar lantarki da sauran ababen more rayuwa. Bayan haka, shin ba wannan ‘Yar’aduwan ba ne a farkon mulkinsa ya bayyana cewa zai farfado da matatun man ba? Me ya canza tun daga hawansa? Shugaban kasarmu ya rude ne?
Abin da ya faru kawai a kan ayyana shirin bunkasa tattalin arzikin shugaban kasar a makon da ya gabata ya tabbatar da tunanin da wasu ke yi a bangarori daban-daban: ba wai shugaban kasar bai san yadda gwamnatoci ke tafiyar da aiki ba ne kawai, amma bai ma san dalilin da ya sa ake kafa gwamnatoci ba. A bara, bai aiwatar da kasafin kudi ba duk da cewa akwai kudin; kuma a bana, ya yi watsi da wasu ayyukan da gwamnati ta amince da su. A tsakiyar rikici irin wanda muka tsinci kanmu a ciki, ana bukatar gwamnatoci da suke da jajircewa. To amma a irin wannan lokaci ne gwamnatinmu ke son ta cire hannu a kan tafiyar da tattalin arzikin kasar nan, sai dai kawai ta zama ‘yar kallo daga nesa.
Yanzu da gwamnatin tarayya ta daina sayen magunguna na asibitocin gwamnati, ta daina gina makarantun da za a koyar da yaranmu, ta kasa samar da tsaron rayuka da dukiyoyi, ta cire tallafin man fetur da sunan ba a yayin haka a zamanin nan kuma ta yanke shawarar fitowa fili ta fada wa al’ummar kasa cewa ba za ta kai dauki ga kasuwar hannayen jari da ke rugujewa ba, shin ba zai fi ma’ana ba, idan aka mayar da gwamnatin hannun masu zuba jari kawai ko a sayar da ita ga wadanda za su saye ta da kudi mai daraja ba? Kodayake wani abokina ya yi saurin tunatar da ni cewa ai an riga an yi hakan ma. Mutanen da ke Aso Rock a yau ba su samu damar shiga wurin da kuri’unmu ba. Da kudi suka sayi fadar shugaban kasa kuma suna nan a can har yanzu duk da mun riga mun san komai. To me zai sa kuwa su zama masu tausayi? In ji shi.