Nijeriya na cikin kasashen da ke fama da matsanancin talauci, kamar yadda wani rahoto na hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, UNDP ta fitar a ranar Alhamis.
Rahoton ya bayyana cewa sama da mutane biliyan daya a duniya na fama da matsanancin talauci, inda lamarin ya fi ta’azzara acikin yara masu tasowa.
- Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Mai Nazarin Duniyar Dan Adam
- Wadanne Sakamako Aka Samu Daga Cinikin Tsakanin Sin Da Kasashen Ketare
Rahoton da aka buga tare da hadin gwiwar kungiyar ‘Oxford Poverty and Human Development Initiative (OPHI)’, rahoton ya kuma jaddada cewa, yawan talauci ya karu sosai a kasashen da ke fama da rikici.
Rahoton kididdigar Talauci na ‘Multidimensional (MPI)’ na shekarar 2024, wanda aka fara gabatarwa tun daga 2010, ya tattaro bayanai daga kasashe 112, wanda ya kunshi yawan mutane biliyan 6.3.
MPI tana amfani da alamomi daban-daban wajen kididdigar talauci, da suka haɗa da rashin isassun gidaje, rashin tsafta, ƙarancin wutar lantarki da man iskar gas na girki, rashin abinci mai gina jiki, da ƙarancin zuwa makaranta.
Daga cikin kasashen da lamarin ya fi shafa, Indiya ce ta zo kan gaba inda mutane miliyan 234 ke cikin matsanancin talauci, sai Fakistan, Habasha, Nijeriya, da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.