Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Oi ya bayyana cewa Nijeriya na fuskantar siyasa mara tabbas.
Peter Obi ya bbayyana hakan ne a ciikin sakonsa na ranar ma’aikata da aka gudanar da ranar Laraba da ta gabata.
- CBN Ya Bayyana Sunayen Bankuna 41 Da Ya Aminta Da Ingancinsu A Nijeriya
- Rashin Tsaro: Majalisa Ta Nemi Sojoji Su Ƙaddamar Da Shiri Na Musamman Don Kakkaɓe Ayyukan ‘Yan Ta’adda A Neja
Haka kuma ya bayyana cewa kasar nan tana ci gaba da fuskantar wasu kalubale da suka hada da matsin tattalin arziki da rashin adalci.
Peter Obi wanda ya kasance tsohon gwamnan Jihar Anambra ne ya ce ‘yan Nijeriya su ci gaba da kyautata zato za a samu saukin rayuwa a nan gaba kadan.
Ya ce, “A duk lokacin da ake fuskantar matsin tattalin arziki da siyasa mara tabbas da kuma rashin adalci, ya kamata mutane su ci gaba da tsayuwa a kan duga-dugansu na yin tsammayin cewa wata rana za a samu sauki a cikin kasarmu Nijeriya.
“Ina tare da ma’aikata wajen yaki da neman ‘yancinku. Ina jinjina da irin kokarinku wajen sadaukarwarku ga iyalanku da tallafa wa al’umma da kuma gudummuwarku wajen ciyar da kasarmu.
“Kamar yadda muke murnan ranar ma’aikata a yau, yana da mutukar muhimmanci mu ci gaba da rubanya kokarinmu wajen samun hadin kai da adalci da samun daidaito ga dukkan ‘yan Nijeriya.
“Ya kamata mu yi alfahari da abubuwan da muka cimma domin mu samu karfin ci gaba da hadin kai da kuma sake karfafa gwirin giwa wajen gina kasarmu da kuma al’umma masu tasowa,” in ji Peter Obi.