Kamfanin Man Fetur na Ƙasa na Nijeriya (NNPCL) ya bayyana cewa ƙasar na burin samun jarin Dala biliyan 60 cikin shekaru biyar zuwa bakwai masu zuwa domin faɗaɗa fannin iskar gas.
Babban Jami’in Gudanarwa na NNPCL, Mista Bayo Ojulari, ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga masu sauraro daga ƙasashe 150 a wajen buɗe taron Gastech Exhibition da Conference da aka gudanar a Milan, Ƙasar Italiya. Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na neman wannan jarin ne don ƙarfafa masana’antu da kuma tabbatar da matsayi mai ƙarfi na Nijeriya a kasuwar makamashi ta duniya.
- Kungiyar Kare Shirye-shiryen Tinubu Ta Nemi A Dakatar Da Shugaban Kamfanin NNPCL
- Matatar Mai Ta Fatakwal Ba Ta Siyarwa Ba Ce – NNPC
A cewarsa, jarin da aka tsara zai mayar da hankali ne wajen haɓaka samar da iskar gas na asali a Nijeriya zuwa biliyan 12 na cubic feet a kowace rana da kuma faɗaɗa ƙarfin masana’antar tace mai domin biyan ƙaruwar buƙatar makamashi da ake samu ta duniya.
“Muna neman aƙalla jarin Dala biliyan 60 cikin shekaru biyar zuwa bakwai masu zuwa, wanda ake buƙata ga masana’antar mai da iskar gas ɗinmu. Wannan ya taƙaita ne a ƙaramin ɓangare kawai. Mun na neman masu zuba jari domin haɓaka samar da kayayyaki,” in ji shi.
Ojulari ya bayyana cewa Dokar Masana’antar Mai da Gas (Petroleum Industry Act – PIA), wadda aka sanya wa hannu a 2021, ta sauya NNPC zuwa kamfani mai iyaka (limited liability company), wanda ya bai wa kamfanin damar samun kuɗaɗen kai tsaye da kuma kafa haɗin gwiwa na duniya.
Ya ce a halin yanzu kamfanin na samar da kimanin ganga miliyan 1.6 na mai a kowace rana (bpd) tare da burin haɓaka samarwa zuwa miliyan 2 bpd nan da shekara ta 2027 da miliyan 3 bpd nan da 2030. Ya haskaka ayyukan da ake gudanarwa a halin yanzu, ciki har da bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), faɗaɗa West African Gas Pipeline zuwa Morocco da Turai, da kuma haɓaka aikin Nigeria LNG.
A cewarsa, Nijeriya tana samar da kashi 60 cikin ɗari na LNG ga Portugal da Sipaniya, kuma a halin yanzu tana kan Train 6, tana gina Train 7 wanda za a kammala a shekara ta 2026, tare da shirin gina Trains 8 da 9. “Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da mafi kyawun harkokin LNG a duniya. Muna son amfani da babbar buƙatar makamashi a yanzu, wadda ake sa ran za ta ƙaru sosai nan gaba,” in ji shi.
Game da makamashi mai tsafta, Ojulari ya ce gwamnati na ƙarfafa amfani da LPG kuma ta ƙaddamar da shirin rarraba silinda miliyan 2 a faɗin ƙasar, yayin da ake kuma aiwatar da shirin canjin motoci da na’urori zuwa Compressed Natural Gas (CNG).
Game da rawar Nijeriya a harkar tsaron makamashi na duniya, ya ƙara da cewa sauye-sauyen siyasa a duniya, kamar yakin Rasha da Ukraine, sun hanzarta aiwatar da ayyukan bututun iskar gas na yanki domin ƙarfafa tsaron makamashi. Shugaban NNPCL ya ce Nijeriya na da filayen mai da iskar gas sama da 200 da ba a haɓaka ba, inda ya bayyana su a matsayin damammaki masu kyau ga masu zuba jari na ƙasashen waje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp