Tattaunawar da ake yi tsakanin kamfanin jiragen saman ‘Ethiopian Airlines’ da jami’an Nijeriya, don kafa kamfanin hadin guiwa da kamfanin ‘Nigeria Air’ da ya rushe.
Rushewar ta biyo bayan tattaunawar da aka shafe watanni ana yi, wanda ke nuna sauyin dabaru ga gwamnatin Nijeriya, kamar yadda shugaban kamfanin jiragen saman Habasha, Mesfin Tasew, ya tabbatar, ya ce Nijeriya, ba ta da sha’awar hada guiwa da wani kamfanin jiragen sama na kasashen waje.
Tsarin dawo da ‘Nigeria Air’ zai ba wa masu zuba hannun jarin Nijeriya su saka kaso 46, gwamnatin Nijeriya kuma kaso 5, da kashi 49 daga kamfanin Ethiopian Airlines.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp