• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Ta Fuskanci Cikas Wajen Karɓo Rancen Dala Biliyan 5 Daga Saudiyya

by Sadiq
5 months ago
Rance

Nijeriya na ƙoƙarin samun rancen Dala biliyan biyar daga ƙasar Saudiyya, amma an samu tsaiko a tattaunawar saboda sauyin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

Wannan rancen ana sa ran cewa kamfanin man fetur na Saudiyya, Aramco, ne zai bayar, kuma Nijeriya za ta biya da ɗanyen mai.

  • Wang Yi Ya Gabatar Da Jawabi Albarkacin “Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa” Karo Na Farko Na MDD
  • Sin Na Maraba Da Karin ‘Yan Kasuwar Ketare Dake Son Gudanar Da Hada-hada Don Cimma Moriyar Juna

Wani rahoto daga kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa faɗuwar farashin ɗanyen mai nau’in Brent daga Dala 82 zuwa Dala 65 tun daga watan Janairu ya sa bankunan da za su taimaka wajen aiwatar da rancen suka fara nuna shakku.

Idan aka ci gaba da wannan tattaunawa, Nijeriya za ta ƙara yawan mai da za ta biya da shi don biyan bashin.

Tatttaunawa kan wannan rance dai ta fara ne tun cikin watan Nuwamban 2024 lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Yarima Muhammad Bin Salman a taron tattalin arziƙi tsakanin Saudiyya da ƙasashen Afrika.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

Amma har zuwa yanzu, babu cikakken bayani daga Gwamnatin Tarayya.

A watan Mayun 2025 ne Tinubu ya miƙa buƙatar samun amincewar majalisa domin karɓar rancen Dala biliyan 21 daga ƙasashen waje, ciki har da Dala biliyan biyar daga Aramco.

Rahoton Reuters bai bayyana sunayen bankunan da za su taimaka ba, amma majiyoyi sun ce ɗaya daga cikin bankunan na nahiyar Afrika ne, sauran kuma daga Gabas ta Tsakiya.

Idan aka cimma yarjejeniyar, wannan zai zama mafi girma daga cikin bashin da Nijeriya ta taɓa karɓa a irin wannan hanya daga Saudiyya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce
Manyan Labarai

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Next Post
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

Nan Ba Da Jimawa Ba Harkar Man Fetur Za Ta Sauya A Nijeriya - Dangote

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.