Gwamnatin Tarayya ta jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yammacin Afirka duk da jawabin da shugaban jamhuriyar Nijar, Abdourahman Tchiani, ya yi a baya-bayan nan wanda Nijeriya ke kallon jawabin a matsayin zargin da shi da tushe ballantana makama.
A wata sanarwar da ministan kula da harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya nuna aniyar Nijeria na tattaunawa domin samu ginshikin mafita mai dorewa.
- Karuwar Cin Zarafi Da Makomar Yara A Nijeriya
- Abuubuwan Da Suka Fi Daukar Hankalin ‘Yan Nijeriya A 2024
Tuggar ya ce sam ko da wasa Nijeriya ba ta da niyyar yin zangon kasa ga tsaron Nijar, a maimakon haka ma ta zabi ta mutunta da kyautata dadadden tarihin da ke tsakanin kasashen biyu.
“A matsayin ‘yan uwanmu kuma makwabtanta, Nijeriya da Nijar suna da jimammen tarihi da al’adun a tsakani, wanda hakan ya kai ga dogon kasuwanci da tattalin arziki,” ya shaida.
Ya ce, wadannan muhimman abubuwan da suka hada kasashen sun wuce a tsaya a yi wasa da su, kuma Nijeriya da Nijar kamar abu guda ne.
“Don haka, zarge-zargen ba su da tushe balle makama, wanda ka iya haifar da tashin hankali marar ma’ana, wanda ka iya haifar da rashin jituwa da barazana ga hadin kan yankinmu.
“Mun jaddada aniyarmu na mutunta tsaron Nijeriya da kimarta daidai yadda yake a tsarin ECOWAS.
“Muna maraba da kuma karfafa budaddiyar tattaunawa mai ma’ana a tsakanin gwamnatocinmu, muna kuma gayyatar shugabannin Nijar da su zo mu hadu tare wajen tattaunawa ta gaskiya don magance matsalolin da suke fuskantarmu.”
Ya kuma ce Nijeriya a shirye take ta hada kai domin karfafa gwiwa wajen yin abubuwan da suka dace wajen kyautata ayyukan jin kai a iyakokin Nijar da Nijeriya.