Gwamnatin tarayya a ranar Larabar da ta gabata ta ce an kwato sama da dala biliyan 1 da aka sace daga asusun gwamnati tun farkon gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya FEC.
Ya ce an mika kadarorin da aka kwato zuwa sassa daban-daban na tattalin arziki da suka hada da hukumar shirye-shiryen rage radadin talauci.
Ya ce gwamnati ta kuma kama laifuka 109 ne kawai kafin zuwan gwamnatin Buhari; yayin da gwamnatin Buhari ta yanke wa sama da mutane 3,000 hukuncin laifi.
Ya kuma ce majalisar FEC ta amince da sabon kundin dabarun yaki da cin hanci da rashawa (2022-2026) don karfafa hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annuti ta kasa.
Majalisar ta kuma amince da cike gibin kasafin kudi na Naira biliyan N14bn na aikin babban titin Kano ta yamma wanda zai hade zuwa Maiduguri da aka baiwa kamfanin Dantata and Sawoe gudanar da aikin.