Kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya da ake wa lakabi da Super Eagles ta lallasa tawagar kwallon kafa ta kasar Sao Tome Principe da ci 6-0.
Wasan shine zagaye na biyu na wasannin share fagen shiga gasar kofin kwallon kafa ta nahiyar Afirka.
A wasan farko da aka buga a tsakannin kasashen biyu, Nijeriya ta samu nasara da ci 10-0.
A wasan na yau Victor Osimhen ne ya jefa kwallaye uku rigis, sai kuma Lukman, Awoniyi da Samuel Chukwuze da kowanensu ya jefa kwallo daya.
An buga wasan a babban filin wasan kwallon kafa dake Uyo a jihar Akwa Ibom.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp