Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) ta samu nasarar lashe kofin ƙasashen nahiyar Afirika na mata bayan doke masu masaukin baƙi Maroko a wasan ƙarshe da ci 3 da 2.
An buga wasan ne a daren ranar Asabar, wanda ya ƙayatar da masu kallo.
- Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa
- Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya
Ƙasar Moroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu a minti na 14 da minti 24.
Amma Nijeriya ta farke duka ƙwallaye biyu kuma ta jefa ta uku a minti na 89 na wasan, da wannan sakamakon Nijeriya ta samu nasarar lashe gasar karo na 10 a tarihi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp