• English
  • Business News
Wednesday, August 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Ta Nemi Kasashe Su Tunkari Matsalolin Gudun Hijira Da Shige Da Fice Gadan-gadan

by Sulaiman
3 years ago
in Labarai
0
Nijeriya Ta Nemi Kasashe Su Tunkari Matsalolin Gudun Hijira Da Shige Da Fice Gadan-gadan
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Nijeriya ta yi kira ga sauran ƙasashe da su haɗa gwiwa domin nemo hanyoyin da za a bi a magance matsalolin da su ka danganci shige-da-fice da gudun hijira.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji Da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta yi wannan kiran a jawabin da ta gabatar a ranar Litinin a wajen Taro na 73 na Babban Kwamitin Gudanarwa na Kwamishinan Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) a birnin Geneva.

  • Ayyukanmu Duk Sun Karade Ko’ina A Fadin Nijeriya —Sadiya Farouq

Mai tallafa wa ministar a aikin jarida, Miss Nneka Ikem Anibeze, ta ruwaito cewa Hajiya Sadiya ta bayyana irin ƙoƙari da kuma da tsare-tsaren da gwamnatin Nijeriya ta ke fito da su domin inganta ayyukan agaji a Nijeriya musamman ma kan batun ‘yan gudun hijira da masu shige-da-fice tsakanin ƙasashe da kuma ‘yan gudun hijira na cikin ƙasa.

Ministar ta yi kira ga ƙasashe masu ruwa da tsaki a lamarin da su guji nuna bambanci da wariyar launin fata domin gina zaman lafiya mai ɗorewa tare da inganta hanyoyin samun abinci ga al’umma mabuƙata.

Ta ce: “Nijeriya ta na kira ga ƙasashe da su haɗa gwiwa tare da haɗa kai da ɗaukar nauyi da zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya musamman a kan yadda matsalar ke shafar ƙasashe inda ‘yan gudun hijira ke fitowa da ƙasashen da ke karɓar su. Wannan ya yi daidai da sadaukarwar mu a matsayin membobin Yarjejeniyar Ƙasashe Kan ‘Yan Gudun Hijira.

Labarai Masu Nasaba

“Ku Yi Murabus Idan Baza Ku Iya Rike Amanar Jama’a ba” – Gargadin Gwamna Abba Ga Kwamishinoninsa

Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya

“Nijeriya ta yabi ƙoƙarin UNHCR. Mu na kuma kira ga UNHCR da sauran masu ruwa da tsaki kan batun shige-da-fice da su ci gaba da su haɗa hannu da gwamnatin Nijeriya domin a daidaita tsare-tsare da manufofin mu na cigaban ƙasa da muradan ta.

“Matsalar da ake samu daga sauyin yanayi a Fadamar Tafkin Chadi ta haifar da ƙarin yawan mutanen da aka tilasta wa barin yankin.”

Ta lura da cewa a cikin ‘yan lokutan nan ambaliya da sauran manyan al’amuran sauyin yanayi sun ba da gudunmawa ga ƙaruwar ‘yan gudun hijira.

Ta ce, “A namu ɓangaren na gwamnati, mu na aiwatar da Shirin Ko-ta-kwana na Samar da Abincin Gaggawa domin inganta shiryawa da ƙarfafawa ga al’umma kamar yadda aka tsara a Tsarin Sendai.”

Hajiya Sadiya ta ce: “Mu na neman a haɗa gwiwa domin a rage tare da shirya zama da sauyin yanayi musamman a wajen batun tilasta wa mutane barin waje.

“Wariyar launin fata da nuna bambanci ba abubuwa ne da za a bar su su samu gindin zama a duniyar mu ta yau ba idan har mu na so mu gina zaman lafiya mai ɗorewa, samar da arziki da kuma inganta sana’o’i da juriya ta yadda za a kyautata ƙasa tare da kare al’umma marasa ƙarfi.”

A ƙarƙashin Yarjejeniya Uku da aka rattaba tsakanin Nijeriya, Kamaru da UNHCR, sama da ‘yan gudun hijira 5,000 ‘yan Nijeriya aka sake dawowa da su cikin ƙasar su bisa amincewar su.

Ta ce a cikin shekaru shidda da su ka gabata, Nijeriya ta samu ƙarin yawaitar masu neman mafaka da ‘yan gudun hijira daga ƙasashe da ke maƙwabtaka da mu.

Yanzu haka Nijeriya ta na mai masaukin baƙi na ‘yan gudun hijira su 84,314 da masu neman mafaka daga ƙasashe sama da 34, ga kuma ƙarin sama da ‘yan gudun hijira 5,000 daga Kamaru waɗanda ba su da rajista, waɗanda su ka iso kwanan nan.

“Akwai ‘yan gudun hijira ‘yan Nijeriya kimanin 341,642 a ƙasashen Nijar, Chadi da Kamaru,” inji ta.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Peng Liyuan Ta Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Karrama Wadanda Suka Yi Fice A Fannin Tallafawa Ilimin Mata

Next Post

Abinda Ya Sa Naki Amincewa Na Wa Obi Mataimaki —Shagari

Related

Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu
Labarai

“Ku Yi Murabus Idan Baza Ku Iya Rike Amanar Jama’a ba” – Gargadin Gwamna Abba Ga Kwamishinoninsa

56 minutes ago
Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya
Manyan Labarai

Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya

2 hours ago
Uwargidar Gwamnan Katsina Ta Nemi A Taimaka Wa Mata Wajen Yaƙi Da Ciwon Nono Da Na Mahaifa
Labarai

Uwargidar Gwamnan Katsina Ta Nemi A Taimaka Wa Mata Wajen Yaƙi Da Ciwon Nono Da Na Mahaifa

6 hours ago
Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa
Labarai

Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa

8 hours ago
Sojoji Sun Kama Mai Yi Wa Boko Haram Safarar Man Fetur A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Mai Yi Wa Boko Haram Safarar Man Fetur A Borno

9 hours ago
Matar Marigayi MKO Abiola, Ta Rasu Tana Da Shekaru 82
Manyan Labarai

Matar Marigayi MKO Abiola, Ta Rasu Tana Da Shekaru 82

10 hours ago
Next Post
Abinda Ya Sa Naki Amincewa Na Wa Obi Mataimaki —Shagari

Abinda Ya Sa Naki Amincewa Na Wa Obi Mataimaki —Shagari

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Za Ta Nuna Goyon Baya Ga Sabbin Masana’antu Ta Hanyar Hada-Hadar Kudi

Kasar Sin Za Ta Nuna Goyon Baya Ga Sabbin Masana’antu Ta Hanyar Hada-Hadar Kudi

August 6, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

“Ku Yi Murabus Idan Baza Ku Iya Rike Amanar Jama’a ba” – Gargadin Gwamna Abba Ga Kwamishinoninsa

August 6, 2025
Sin Ya Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Aiwatar Da Mataki Mai Hadari A Zirin Gaza

Sin Ya Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Aiwatar Da Mataki Mai Hadari A Zirin Gaza

August 6, 2025
Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya

Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya

August 6, 2025
Sin Ta Samar Da Yuan Biliyan Daya Domin Ayyukan Jin Kai Sakamakon Ibtila’in Ambaliyar Ruwa

Sin Ta Samar Da Yuan Biliyan Daya Domin Ayyukan Jin Kai Sakamakon Ibtila’in Ambaliyar Ruwa

August 6, 2025
Uwargidar Gwamnan Katsina Ta Nemi A Taimaka Wa Mata Wajen Yaƙi Da Ciwon Nono Da Na Mahaifa

Uwargidar Gwamnan Katsina Ta Nemi A Taimaka Wa Mata Wajen Yaƙi Da Ciwon Nono Da Na Mahaifa

August 6, 2025
Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa

Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa

August 6, 2025
Sojoji Sun Kama Mai Yi Wa Boko Haram Safarar Man Fetur A Borno

Sojoji Sun Kama Mai Yi Wa Boko Haram Safarar Man Fetur A Borno

August 6, 2025
Matar Marigayi MKO Abiola, Ta Rasu Tana Da Shekaru 82

Matar Marigayi MKO Abiola, Ta Rasu Tana Da Shekaru 82

August 6, 2025
Remi Tinubu Ta Bai Wa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa A Neja Tallafin N1bn

Remi Tinubu Ta Bai Wa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa A Neja Tallafin N1bn

August 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.