Hukumar kididdaga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa Nijeriya ta samu raguwar kudaden shiga da kashi 3.10 a 2022, daga kashi 3.40 da aka samu a 2021.
Hukumar NBS ta bayyana cewa fannin noma da masana’antu ya ragu a 2022, yayin da a baya fannonin suka samu bunkasa a duk shekarun da suka gabata.
- Da Dumi-Dumi: Sergio Ramos Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Sifaniya Kwallo
- Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Karfafa Aikin Nazari
A cikin sulisin 2022, kudaden shiga ya karu da kashi 3.52 a zahiri. An samu karuwan ne sakamakon bangaren ayyuka ci gaban, wanda ya sami bunkasa da kashi 5.69 da ya bayar da gudummawar kashi 56.27 na jimillar kudaden shiga.
A cikin rahotonta na jimlar kudaden shigan Nijeriya a sulisin 2022, NBS ta ce, “Nijeriya ta kara samun kudaden shiga da kashi 3.52, a hakikanin gaskiya a rubu’i na hudu na 2022, biyo bayan karuwar kashi 2.25 a kwatan 2022, yayin da aka samu kashi 3.98 a farkonm wata hudun 2021.
“A cikin farkon watanni hudun 2022 ya kasance mafi yawa daga bangaren ayyukan fannoni daban-daban, wanda ya sami kashi 5.69 tare da bayar da gudummawar 56.27 daga cikin kudaden shigan da Nijeriya ke samu.”
Hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana cewa, fannin noma ya karu da kashi 2.05 kacal a cikin 100 da aka yi nazari a kai, saboda ambaliyar ruwa da aka fuskanta a fadin kasar nan.
Hukumar ta kara da cewa, “Har yanzu ana fuskanci kalubale a bangaren masana’antu wanda aka samu -0.94 bisa dari, wanda ya bayar da gudummawa kalilan a cikin kudaden shigan Nijeriya a sulisin 2022, wanda bai kai wanda aka samu a 2021.