Nijeriya ta shigo da man fetur da ya kai na naira tiriliyan 12.48 a shekarar 2024, kamar yadda rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ya nuna.
Rahoton ya bayyana cewa a kashin farko na shekarar, an shigo da fetur na naira tiriliyan 2.63, sai na tiriliyan 3.22 a kashi na biyu, sannan tiriliyan 3.32 a kashi na uku, da kuma tiriliyan 3.3 a kashi na huɗu.
Binciken ya kuma nuna cewa Nijeriya ta yi cinikayya da ƙasashen waje da ya kai naira tiriliyan 138.
Sannan, an kashe tiriliyan 60.5 wajen shigo da kayayyaki, yayin da aka samu tiriliyan 77.4 daga kayayyakin da aka fitar.
A cikin kayayyakin da aka fi shigo da su, tataccen man fetur ne ke kan gaba, yayin da fitar da ɗanyen mai ya fi yawa a kayayyakin da Nijeriya ke sayar wa ƙasashen waje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp