Nijeriya ta ce hukumomin sojin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso wadanda ba zababbun al’umman kasar ba ne, sun zalunci al’ummarsu yayin da suka dauki matakin hadin gwiwa na ficewa daga ECOWAS.
Nijeriya wadda ita ce ke shugabantar ECOWAS, ta yi tsokaci a karon farko kan sanarwar da kasashen uku karkashin jagorancin mulkin soji suka fitar a ranar Lahadi cewa, sun fice daga kawancen yankin da aka kwashe kusan shekaru 50 ana yi.
- Nasarata A Kotu Ta Nuna Adalcin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Fintiri
- Shari’ar Fintiri da Binani: Yau Jama’ar Adamawa Za Su San Matsayinsu A Kotun Koli
Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce wadanda ke neman ficewa daga ECOWAS ba suna yi da kyakkawar manufa ba ne.
Ya zuwa yanzu dai ECOWAS ba ta ce uffan ba kan matakin ba, wanda zai iya kara raunana kungiyar a kokarin da ta ke yi na dakile yunkurin juyin mulkin dimokuradiyya a yankin Yammacin Afirka.
Tun da farko dai ma’aikatun harkokin wajen Mali da Nijar sun sanar da ECOWAS matakin da suka dauka.
Nijeriya ta ce har yanzu tana so ta ci gaba da hulda da kasashen uku.
Matakin ficewar nasu, wanda aka sanar a cikin wata sanarwar hadin gwiwa a lokaci guda a gidajen talabijin na kasar, wani nakaso ne ga yunkurin hadewar kungiyar, bayan ta dakatar da juyin mulkin uku da ya biyo baya.